N500,000: Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Tattaunawa kan Karin Albashi

N500,000: Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Tattaunawa kan Karin Albashi

  • Gwamnatin Tarayya ta ce ta shirya dukkan matakan da suka dace domin fara tattaunawar sabon mafi karancin albashi, yayin da wa’adin N70,000 zai kare
  • Babban Sakataren Ma’aikatar Kwadago da Ayyukan yi ta Tarayya, Kamil Shoretire, ya bayyana hakan yayin wani taron yini guda kan ayyukan ma’aikatar
  • Kungiyar kwadago ta kuma fara matsa lamba kan neman a kara mafi karancin albashi zuwa N500,000 tare da rage farashin litar man fetur zuwa N500

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta ce dukkan matakan da suka dace suna kan hanya domin fara tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata, bayan da aka tsara sake nazari kan albashin N70,000 a shekara mai zuwa.

Babban Sakataren Ma’aikatar Kwadago da Ayyukan yi ta Tarayya, Kamil Shoretire, ne ya bayyana hakan yayin wani taron yini guda da aka gudanar kan ayyukan ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Gwamna zai yi rabon tsabar kudi har Naira biliyan 6 ga talakawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana wani jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar karin albashin ma'aikata

AIT ta rahoto cewa Shoretire ya ce gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen da suka dace domin sake duba mafi karancin albashin ma’aikata da ake biya a halin yanzu.

Ya bayyana hakan ne yayin da bangaren kwadago na Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnati ke neman a kara mafi karancin albashi zuwa N500,000.

Kungiyar ta kuma bukaci a rage farashin man fetur a gidajen mai zuwa N500 kan kowace lita.

Martanin Najeriya ga korafin ILO

Babban Sakataren ya kuma bayyana cewa Najeriya ta cika wa’adin ranar 1 ga Satumba da Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) ta sanya mata domin mayar da martani kan wani rahoto da ma’aikatan Afirka suka gabatar.

Rahoton ya zargi Najeriya da gaza warware wasu batutuwan da suka shafi Kungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Najeriya (NURTW), Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a Edo, da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (TUC) a Legas da sauran batutuwa.

Kara karanta wannan

Sultan ya kausasa harshe kan zubar da jini, ya yi kira ga Tinubu

The Sun ta wallafa cewa Shoretire ya ce Najeriya ta kuma mayar da martani kan batun gazawar aiwatar da Yarjejeniyar ILO mai lamba 187.

Shugabannin kwadago a Najeriya
Shugabannin NLC, TUC a wajen zanga-zanga. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Batun mutuwar mutum 37

A wani bangare na bayaninsa, Shoretire ya ce gwamnatin tarayya a shirye take ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin gano hakikanin abin da ya haddasa mutuwar masu hakar ma’adinai 37 a hannun NSCDC a jihar Niger.

Ya ce Sashen Binciken Ma’aikatu na Ma’aikatar Kwadago a shirye yake ya yi aiki tare da kwamitin da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Ojo, ya kafa domin binciken lamarin.

Ya ce hadin gwiwar zai taimaka wajen gano abubuwan da suka faru kafin mutuwar mutanen da ke tsare a wurin.

Gwamna na biyan N500,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya ce gonarsa tana biyan ma’aikatan da suka kammala jami’a mafi karancin albashi na N500,000 duk wata.

Gwamnan ya bayyana harkar noma, musamman kiwon dabbobi, a matsayin wata babbar dama ta samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce albashin da ake biyan ma’aikata a gonarsa ya fi abin da wasu ma’aikatan gwamnati ke samu, inda ya ce hakan na nuna irin damar da kamfanonin noma masu zaman kansu ke da ita wajen samar da ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng