Gwamnati Ta Sauya Dabara, Ta Cafke Kasurgumin Jagoran 'Yan Ta'adda
- Gwamnatin Tarayya ta ce haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri ya taimaka wajen yaki da matsalar rashin tsaro
- Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kama babban dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo da mataimakinsa ba tare da an harba ko da harsashi ɗaya ba
- Gwamnati ta ce tana ƙara kayan aikin soji tare da kusantar da rundunonin soja zuwa wuraren da ake gudanar da ayyukan tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce ƙara haɗin gwiwa da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri ya taimaka wajen kama jagoran 'yan ta'adda.
Ta ce hadin gwiwar ya taimaka wajen kama Mamuda, wanda ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin ’yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a duniya.

Source: Twitter
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, 24 ga watan Satumban 2026 a Abuja yayin wani taron manema labarai da aka shirya gabanin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, cewar rahoton Punch.
An kama Mamuda ba tare da an yi harbi ba
Idris ya ce kama Mamuda da babban jami’in da yake aiki tare da shi ya nuna yadda musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron Najeriya ke ƙara inganta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
“Yayin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mun ga ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na leƙen asiri."
“Wannan ya taimaka wajen kama ɗaya daga cikin ’yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a duniya, wanda ake kira Mamuda, da babban mataimakinsa. A yau, Mamuda da babban mataimakinsa suna fuskantar shari’a a kotu,” in ji ministan.
Ya ƙara da cewa an kama mutanen ne ba tare da musayar wuta ko harbin bindiga ba.
Amurka da Turai sun sanya tukuicin kama su
Ministan ya ce wasu ƙasashen duniya, ciki har da Amurka da ƙasashen Turai, sun sanya tukuicin kuɗi ga duk wanda ya taimaka wajen kama mutanen.
“Waɗannan mutane ne da ƙasashe kamar Amurka da Turai suka sanya tukuicin kuɗi domin a kama su. Amma a yau, an kama su ba tare da an harba ko da harsashi ɗaya ba,” in ji shi.
A cewar Idris, lamarin na nuna irin haɗin gwiwa da musayar bayanan sirri da ke gudana tsakanin rundunar soji da hukumomin leƙen asiri.
Ya ce hakan na taimakawa wajen ƙara inganta yadda jami’an tsaro ke tunkarar ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Gwamnati ta ce har yanzu akwai ƙalubalen tsaro
Sai dai ministan ya amince cewa Najeriya ba ta gama shawo kan matsalolin tsaron da suka dade suna addabarta ba.
Ya ce ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka na ci gaba da zama abin damuwa a ƙasar.

Kara karanta wannan
El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun kashe kwamanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ne sun kai wani mummunan hari kan al’ummar Wumbi da ke ƙaramar hukumar Kala-Balge a Jihar Borno.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani kwamandan ’yan sa-kai da fararen hula huɗu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Asali: Legit.ng

