Trump Ya Shan Kunya da aka kai Shi Gaban Alkali kan Taba 'Yan Jarida

Trump Ya Shan Kunya da aka kai Shi Gaban Alkali kan Taba 'Yan Jarida

  • Wani alkalin kotun tarayya a Amurka ya umarci gwamnatin Shugaba Donald Trump da ta gaggauta maido da izinin aikin ’yan jaridar CNN, POLITICO da MS NOW
  • Alkalin ya bayar da umarnin ne bayan kafafen yada labaran uku sun shigar da karar hadin gwiwa kan matakin da gwamnatin Trump ta dauka na soke izinin ’yan jaridarsu
  • Timothy Kelly ya ce ’yan jaridar 78 za su ci gaba da samun izinin shiga Fadar White House na akalla makonni biyu yayin da ake ci gaba da sauraron karar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Wani alkalin kotun tarayya a Amurka, Timothy Kelly, ya umarci gwamnatin Shugaba Donald Trump da ta maido da izinin shiga Fadar White House ga ’yan jaridar CNN, POLITICO da MS NOW.

Kara karanta wannan

An yi zaman ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin Amurka da Iran, Trump ya magantu

Kelly ya bayar da umarnin ne da sanyin safiyar Alhamis, inda ya amince da bukatar wucin gadi da kafafen yada labaran suka gabatar a matsayin wani bangare na karar da suka shigar kan soke izinin ’yan jaridarsu.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Alkali ya takawa Trump burki

Politico ta wallafa cewa alkalin ya bayar da umarnin hana gwamnatin aiwatar da matakin dakatar da kafafen yada labaran na tsawon kwanaki 14, tare da bukatar a maido da katunan izinin shiga Fadar White House ga ’yan jaridar da abin ya shafa.

Ya ce bukatar kare aikin jarida cikin ’yanci na bukatar a dauki matakin gaggawa yayin da kotu ke ci gaba da duba karar.

Kafafen yada labaran sun ce matakin gwamnatin ya saba wa kundin tsarin mulkin Amurka, musamman hakkokin ’yancin aikin jarida da kuma hakkinsu na samun damar kare kansu kafin a dauki mataki a kansu.

Dalilin da alkalin ya kawo

A hukuncin nasa, Kelly ya nuna shakku kan hujjar gwamnatin cewa an soke izinin kafafen yada labaran ne saboda matsalolin tsaron kasa.

CNN ta rahoto cewa Alkalin ya ce bayanan da aka gabatar a gaban kotu ba su nuna cewa damuwar tsaron kasa ce ta jawo soke izinin ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabuwar matsala ta kunno kan Trump a Amurka

Ya kuma ce wasu daga cikin rahotannin da gwamnatin ta ambata sun kasance tsofaffi, yayin da ba a gabatar da hujjar da ke nuna cewa rahotannin sun kunshi bayanan sirri ko kuma sun yi illa ga tsaron kasa ba.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka na yi wa jama'a bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kelly ya kara da cewa Donald Trump ya fi mayar da hankali kan zargin rashin gaskiya da kuma mummunan yanayin rahotannin kafafen yada labaran lokacin da ya sanar da dakatar da su, maimakon ambaton matsalar tsaron kasa.

Gargadin da kotu ta yi

Kelly ya ce gwamnatin Amurka ta gaza bai wa ’yan jaridar sanarwar da ta dace ko kuma damar bayyana matsayinsu kafin a soke izinin shiga Fadar White House.

Ya bayyana cewa irin wannan mataki na iya tauye hakkin wadanda abin ya shafa na tsarin doka na adalci.

Lauyan kafafen yada labaran uku, Theodore Boutrous Jr., ya yi maraba da hukuncin, yana mai cewa matakin ya kare ’yancin aikin jarida, tsarin doka da kuma ka’idojin shari’a.

Iran ta caccaki Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce kasarsa ba za ta mika wuya ba bayan kusan watanni bakwai na yakin da Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Trump ya bukaci 'yan Amurka da ke Iran su dauki wani matakin gaggawa

Pezeshkian ya mayar da martani ne kan barazanar Trump ta cewa zai halaka Iran idan ba a cimma yarjejeniya cikin gaggawa ba, inda ya ce matsin lamba da takunkumi za su kara karfafa al’ummar Iran.

Ya kuma ce duk wata yarjejeniya dole ta kunshi kawo karshen toshe hanyoyin da ke hana jiragen ruwan Iran amfani da mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng