Kwankwaso Ya Jawo wa Kansa Rigima da Ya Taba Gwamnan Benue

Kwankwaso Ya Jawo wa Kansa Rigima da Ya Taba Gwamnan Benue

  • Mai magana da yawun Gwamnan Benue ya zargi Rabiu Kwankwaso da tsoma baki cikin harkokin siyasar jihar
  • Tersoo Kula ya ƙi amincewa da sukar Kwankwaso kan Gwamna Hyacinth Alia, yana mai cewa kalaman nasa ba su kamata ba
  • Kula ya kuma zargi magoya bayan Peter Obi da shirya yadda ziyarar Obi zuwa Benue ta gudana domin ɓata sunan Gwamna Alia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Makurdi, jihar Benue - Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Benue, Tersoo Kula, ya mayar wa Rabiu Kwankwaso, martani kan kalaman da ya yi game da rikicin siyasa tsakanin Gwamna Hyacinth Alia da George Akume.

Kula ya zargi Kwankwaso da tsoma baki cikin harkokin siyasar Benue, inda ya bukaci tsohon gwamnan ya mayar da hankali kan ƙalubalen siyasar da ke gabansa a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya tsokano fada, Kwankwaso ya yi masa raddi mai zafi

Gwamnatin Benue ta yi wa Kwankwaso martani
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sanarwar Tersoo Kula da jaridar The Punch ta samu ranar Laraba, 23 ga watan Satumban 2026 ta biyo bayan wata hira da Kwankwaso ya yi.

A yayin hirar, Kwankwaso ya bayyana rashin jituwar Alia da Akume a matsayin “abin takaici wanda bai kamata ba”.

Wane martani aka yi wa Kwankwaso?

Kula ya yi watsi da sukar da Kwankwaso ya yi wa Gwamna Alia, yana mai bayyana kalaman tsohon gwamnan a matsayin “zagi mara dacewa kuma ba shi da hujja”.

Ya ce irin wannan magana ba ta taimaka wajen bunƙasa tattaunawar siyasa ba.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce matsayin Kwankwaso ya samo asali ne daga abin da ya kira “ƙiyayya da ba ta dace ba” da ta biyo bayan cece-kucen da ya taso kan ziyarar Peter Obi zuwa Benue.

‘An shirya ce-ce-kucen ziyarar Obi’

Kula ya zargi Kwankwaso da nuna fushi saboda yadda aka shigar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, cikin Benue ba tare da cikakken tsari ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gano abin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wahala bayan cire tallafin fetur

“Mun fahimci ƙiyayyar da yake da ita ga Gwamna Alia. Yana fushi ne saboda an shigar da maigidansa, Peter Obi, cikin Benue ba tare da kyakkyawan tsari ba, sannan ya zargi gwamnan da lalata ziyarar,” in ji Kula.

Ya kuma yi zargin cewa an shirya ce-ce-kucen da ya biyo bayan ziyarar Obi ne domin ɓata sunan Gwamna Alia a siyasance.

“Wannan wasan kwaikwayon na Obi an shirya shi ne gaba ɗaya daga mutanen da ke son ɓata sunan Gwamna Alia,” in ji shi.

Kula ya ƙara da cewa idan Kwankwaso bai fahimci hakan ba, to hakan na sa su tambayar ko tsohon gwamnan yana fahimtar siyasar yankin.

Ya bukaci Kwankwaso ya mai da hankali kan Kano

Mai magana da yawun Gwamnan Benue ya karkata martaninsa zuwa Kano, inda ya ce tsohon gwamnan na da isassun ƙalubalen siyasa a jiharsa da ya kamata ya mayar da hankali a kansu.

“Ya kamata wani ya gaya wa tsohon Gwamnan Kano cewa maimakon ya tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Benue ko ya yi zarge-zarge marasa tushe kan alaƙar Gwamna Alia da Sanata George Akume, ya kamata ya mai da hankali kan ƙalubalen siyasar da ke gabansa a Kano,” in ji Kula.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya ya sauya sheka, ya bi tafiyar su Kwankwaso a NDC

Ya kuma yi nuni da zaɓen cike gurbin Majalisar Dokokin Jihar Kano na baya-bayan nan a matsayin ɗaya daga cikin batutuwan siyasa da ke gaban Kwankwaso a jiharsa.

Gwamna Alia ya yi wa Kwankwaso martani
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia Hoto: Fr Rev Hyacinth Iormem Alia
Source: Twitter

Kwankwaso ya yi magana kan wahalhalu a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan wahalhalu a Najeriya.

Kwankwaso ya ce Tinubu ya cire tallafin bayan hawansa kan mulki ba tare da samar da matakan da za su rage wa ’yan Najeriya radadin da matakin zai iya haifarwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng