Magana Ta Kare, Amurka Ta Gudanar da Bincike kan Zargin Tinubu da Safarar Miyagun Kwayoyi
- Hukumar FBI ta Amurka tabbatar cewa an taɓa gudanar da bincike kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da laifuffukan safarar miyagun ƙwayoyi
- Ta ce kotun Amurka ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa samun amincewar hukuma kan binciken da aka gudanar a kan Tinubu
- Sai dai hukuncin kotun bai tabbatar da cewa Tinubu ya aikata laifin safarar ƙwayoyi ko kuma an taɓa yanke masa hukunci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Amurka - Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta tabbatar cewa ta gudanar da bincike kan zargin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da safarar miyagun kwayoyi tun a shekarar 1990.
An ce FBI ta bayyana hakan ne a wata takardar da aka gabatar a matsayin rantsuwa a wata kotun tarayya ta Amurka.

Source: Getty Images
FBI ta taba bincikar Bola Tinubu
Daily Trust ta ruwaito cewa an gabatar da takardar ranar 28 ga Agusta, 2026, a gaban Kotun Gundumar Amurka ta yankin Columbia.

Kara karanta wannan
Ana batun rahoton Tinubu, Amurka ta saki sunaye da hotunan 'yan Najeriya 4 da suka tafka laifi
Hakan wani ɓangare ne na ci gaba da shari’ar da aka shigar ƙarƙashin dokar FOIA, wadda ke neman samun bayanan FBI da suka shafi Tinubu.
A cikin takardar, FBI ta ce bayanan da suka dace da buƙatar an tattara su ne yayin binciken da hukumar ta gudanar kan wasu mutane da dama bisa zargin laifukan safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta kuma ce kotun ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa samun amincewar hukuma kan gudanar da bincike a kan Bola Tinubu.
Hukuncin kotun Amurka
Sanarwar FBI ta biyo bayan hukuncin da Alkalin Kotun Amurka, Beryl Howell ta yanke a watan Afrilu 2025.
Alkalin ta ce FBI da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Amurka (DEA) ba za su sake dogaro da abin da ake kira “Glomar” ba wajen ƙin tabbatarwa ko musanta fitar da bayanan da suka shafi binciken.
Howell ta ce hukumomin sun kasa gabatar da isassun dalilan kare sirrin mutum da za su ba su damar ɓoye cewa an gudanar da binciken laifi kan Tinubu.
Sai dai hukuncin bai tabbatar da cewa Tinubu ya aikata laifin safarar miyagun ƙwayoyi ba, kuma bai nuna cewa an taɓa yanke masa hukunci kan wani laifi ba.
Abubuwan da ake so a fitar kan Tinubu
Sabuwar sanarwar ta shafi buƙatun sakin bayanan binciken Tinubu da wani lauya Ba’amurke mai fafutukar tabbatar da gaskiya, Aaron Greenspan, ya gabatar ƙarƙashin FOIA.
Daga cikin bayanan da ya nema akwai “cikakken fayil ɗin FBI na Bola Ahmed Tinubu” da kuma bayanan tambayoyin FBI 302 da suka shafi Tinubu a cikin shari’a mai lamba 245-IP-71386-UUUUUU tsakanin 1992 da 1993.

Source: Twitter
Buƙatun Greenspan na daga cikin wani faɗaɗɗen yunƙuri na samun bayanai game da wata hanyar safarar hodar iblis ta Chicago wadda ta yi aiki a farkon shekarun 1990.
Kamfanin Von Batten-Montague-York, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ɗauka haya gabanin zaɓen 2027, ya wallafa wasu sassan sanarwar FBI.
Kamfanin ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X cewa yana nazarin dimbin bayanan da ya karɓa daga FBI tare da ɓoye wasu sassan inda ya ga hakan ya zama dole.
Abin da ya hana kama Tinubu a Amurka
Kun ji cewa lauyan shugaban kasa, Bola Ahmed Tonubu, Wole Afolabi, ya yi karin haske kan zargin da ake wa shugaban kasa kan safarar miyagun kwayoyi a Amurka.
Lauyan ya ce da a ce akwai hujjar da ke alakanta shugaban da safarar miyagun kwayoyi a Amurka, da hukumomin kasar sun kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Asali: Legit.ng

