Bayan Kwanaki 61, An Ceto Shugaban Karamar Hukumar da Ya Fada Tarkon Yan Bindiga
- An ceto Shugaban Karamar Hukumar Bungudu, Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane 4 da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda
- Sojojin Operation Fansan Yamma sun karɓi mutanen tare da kai su asibitin sojoji domin kula da lafiyarsu
- Bayanai sun nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto daga hannun yan bindigar ya riga ya koma wurin iyalansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun ceto Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Abdullahi.
Dakarun sojojin sun ceto ciyaman din tre da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, bayan sun tsere daga hannun ’yan ta’adda da sanyin safiyar Laraba.

Source: Facebook
Mai magana da yawun Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Alhamis kuma aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Iska mai ƙarfi ta haddasa hatsarin jirgi, mata da dama sun rasa rayukansu a Najeriya
Ciyaman da mutum 4 sun kubuta
Danja ya ce mutanen sun tsere ne a yankin Karamar Hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, inda daga bisani sojoji suka shiga daji suka dauko su.
Ya ce an yi garkuwa da Hon. Abdullahi daga gidansa da ke garin Bungudu a watan Yuli 2026, lamarin da Rundunar Yaki da Ta’addanci ta riga ta fitar da sanarwa a kansa.
A cewarsa, mutanen sun tsere ne yayin da sojoji ke gudanar da wani samame bisa bayanan sirri a kan wani wuri da ake zargin ’yan ta’adda ne a yankin.
“Dakarun da aka jibge a yankin ne suka karɓe su. An ba su kariyar tsaro sannan aka kwashe su zuwa wani asibitin sojoji, inda suke karɓar magani tare da gudanar da gwaje-gwaje da kuma yi musu tambayoyi na yau da kullum,” in ji shi.
An sake haɗa ɗaya da iyalansa
Danja ya ce an riga an sake haɗa ɗaya daga cikin mutanen da iyalansa, yayin da ake shirye-shiryen tabbatar da dawowar sauran mutanen cikin aminci ga iyalansu da gwamnatin Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira
“Rundunar Yaki da Ta’addanci tana yaba wa jajircewa, juriyar wahala da ƙudurin waɗanda abin ya shafa wajen samun ’yancinsu bayan shafe tsawon lokaci a hannun masu garkuwa.
“Haka kuma tana yaba wa dakarun bisa taka-tsantsan da ƙwarewar da suka nuna wajen karɓar mutanen da kuma tabbatar da tsaronsu.
“Dawowar mutanen abin farin ciki ne ga iyalansu da al’ummar Karamar Hukumar Bungudu da Jihar Zamfara baki ɗaya,” in ji shi.

Source: Twitter
Ya tabbatar da cewa dakarun Operation Fansan Yamma za su ci gaba da gudanar da samame da ayyukan tabbatar da iko a yankunan domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da kuma kare al’ummomi.
Sojoji sun ceto daliban jami'ar FUDMA
A wani labarin, kun ji cewa sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Dayi-Malumfashi da ke jihar Katsina.
Mutanen da aka ceto sun haɗa da ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma da kuma wani direban motar haya.
Asali: Legit.ng