Yadda Tinubu ke Kokarin Tabbatar da Dimukradiyya da Tsaya da Kafafunta
- Ministan Tsaro Christopher Musa ya bayyana kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi a bangaren tsaro
- Musa ya ce gwamnati na ƙarfafa rundunar soji, zamanantar da kayan tsaro da amfani da fasahohin zamani domin tunkarar barazanar tsaro
- Ministan ya bayyana cewa barazanar tsaro na shafar ƙasa, teku, sararin sama da yanar gizo, yana mai buƙatar haɗin gwiwar hukumomin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bai wa tsaron ƙasa fifiko domin kare ikon Najeriya.
Ya ce hakan zai taimaka wajen kare cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma samar da yanayin da zai ba da damar ci gaban ƙasa.

Source: Facebook
Musa ya bayyana hakan ne a Abuja yayin buɗe taron tattaunawar manufofi karo na biyu, mai taken “Ƙarfafa Iyakokin Ƙasa", cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND
Ministan tsaro ya yaba wa Tinubu
Ma’aikatar Tsaro ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar 'Saban Media Services' domin tattauna batutuwan tsaro da dabarun kare ƙasa.
Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya ci gaba da jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ƙarfafa tsaron ƙasa da bai wa sojoji kayan aiki.
Ya ce ana samar da abubuwan da ake buƙata domin rundunar sojin Najeriya ta samu damar kare ƙasar da kuma tinkarar barazanar tsaro.
“Wannan tsarin dabarun ya fahimci cewa Najeriya mai tsaro da kwanciyar hankali na da muhimmanci wajen kare ikon ƙasa da cibiyoyin dimokuraɗiyya.”
“Har ila yau, tsaro da kwanciyar hankali na taimakawa wajen bunƙasa ƙasa da kare muradun Najeriya a fannoni daban-daban.”
A cewar Musa, Ma’aikatar Tsaro na mai da hankali kan ƙarfafa ƙarfin tsaro, zamanantar da sojoji da tabbatar da shiryawarsu.
Ya ce ana kuma tabbatar da cewa rundunar soji na cikin kyakkyawan shiri domin fuskantar buƙatun yanayin tsaron da ke sauyawa.
Musa ya ce taron tattaunawar manufofi na shekarar 2026 ya zo ne a lokacin da yanayin tsaron Najeriya ke buƙatar sabbin dabaru.
Ya ce ana buƙatar sauya tsarin hukumomi, da kuma ci gaba da jajircewar ƙasa wajen tunkarar matsalolin tsaro.
A cewarsa, sauyin yanayin barazanar tsaro a duniya na buƙatar Najeriya ta riƙa sake duba ƙarfinta da kuma shirye-shiryenta.
Ya ƙara da cewa ƙasar na buƙatar kasancewa a gaba wajen fahimtar abubuwan da ka iya shafar muradunta na ƙasa.
Ya ce taron ya samar da damar zurfafa tattaunawa kan makomar tsarin tsaro da dabarun kare Najeriya.
“Taken taron na bana ya dace matuƙa da haƙiƙanin matsalolin tsaron da ke fuskantar ƙasarmu a wannan lokaci.”
“Taken ya nuna buƙatar samar da tsarin tsaro da zai iya sauya dabara bisa ga barazanar da ke tasowa, tare da amfani da fasaha.”
Musa ya ce hakan zai ƙarfafa cibiyoyin da ke kula da tsaron ƙasa da kuma tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa iyakokin dabarun tsaron Najeriya na ƙara fuskantar ƙalubale a ƙasa, teku, sararin sama da kuma yanar gizo.
Ya ce magance waɗannan matsaloli na buƙatar tsarin tsaro mai haɗin gwiwa, ingantaccen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.
Ya ƙara da cewa dole ne rundunar soji da sauran hukumomin tsaro su ƙarfafa haɗin kai da aiki tare domin samun sakamako mai kyau.
“Tsarin tsaronmu dole ne ya kasance mai saurin daidaitawa da hangen nesa, tare da ikon hango barazana, mayar da martani da kare iyakokin Najeriya.”
MURIC ta bukaci ministan tsaro ya yi murabus
An ji cewa MURIC ta ce an kashe mutane 43 da limami, sannan aka sace wasu 19 a jihar Sokoto cikin makonni uku Ƙungiyar ta zargi.
Sojojin Najeriya da gazawar kare al’ummar jihar tare da neman a samar da ingantaccen tsarin tsaro MURIC ta bukaci.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya kawo sauyi ko ya gabatar da takardar murabus.
Asali: Legit.ng

