Jigo a APC Ya Rubuta Zungureriyar Wasika ga Tinubu kan Ci Gaba da Tsare El Rufai

Jigo a APC Ya Rubuta Zungureriyar Wasika ga Tinubu kan Ci Gaba da Tsare El Rufai

  • Denge Onoh ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya sa baki kan shari’o’in da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ke fuskanta
  • Onoh ya ce bai kamata a manta da gudunmawar El-Rufai wajen nasarar APC da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba
  • Ya yi nuni da Sashe na 174 da 175 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 a matsayin hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon kakakin yankin Kudu maso Gabas na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Denge Josef Onoh, ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu kan Nasir El-Rufai.

Jigon na APC ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan shari’o’in da tsohon gwamnan na jihar Kaduna ke fuskanta.

El-Rufai na ci gaba da zama a tsare
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Malam Nasir El-Rufai Hoto: Bayo Onanuga, Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Onoh, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar tsofaffin ’yan majalisar dokokin jihar Enugu, ya yi wannan kira ne a wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 24 ga Satumba 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Duk da yana tsare, Atiku ya nada Malam Nasir El Rufai a kwamitin yakin neman zaben ADC

An aika wasiƙar zuwa ga Shugaba Tinubu ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Onoh ya nemi a fifita sulhu

Wasiƙar ta buƙaci Tinubu ya fifita sulhu da kishin ƙasa wajen tunkarar lamarin tsohon gwamnan.

El-Rufai na fuskantar shari’o’i da suka haɗa da ƙarar da Hukumar DSS ta shigar kan zargin kutse ba bisa ƙa’ida ba cikin sadarwar wayar tarho.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Oktoba domin yanke hukunci kan buƙatar El-Rufai ta cewa babu wata hujjar da za ta sa a ci gaba da shari’ar a kansa.

Ya tuna da rawar El-Rufai a APC

Onoh ya ce bai kamata a manta da gudunmawar da El-Rufai ya bayar wajen gina APC da kuma yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

Ya ce tsohon gwamnan na daga cikin muhimman mutane da suka taka rawa wajen yaƙin neman zaɓen da ya kai Tinubu ga nasarar zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya tsokano fada, Kwankwaso ya yi masa raddi mai zafi

Onoh ya bayyana halayen El-Rufai

Onoh ya amince cewa El-Rufai mutum ne mai wahalar aiki da shi, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai tsaurin ra’ayi kan abubuwan da ya yarda da su.

Sai dai ya ce irin waɗannan halaye sun kuma nuna amincinsa ga abin da ya yi imani da shi da kuma mutanen da yake ɗauka a matsayin abokansa.

Ya kuma nuna damuwa kan zargin cewa wasu abokai da abokan hulɗar El-Rufai sun nisanta kansu da shi saboda la’akari da siyasa.

Onoh ya ce ba ya son yin shiru saboda matsin lambar siyasa, yana mai cewa har yanzu yana kallon El-Rufai a matsayin abokinsa wanda gudunmawarsa wajen gina ƙasa ta cancanci a amince da ita.

Ya kawo misalan sulhun siyasa

Onoh ya roƙi Tinubu ya yi la’akari da darussan tarihi game da sulhun siyasa. Ya kawo misalin Julius Caesar da manufofinsa na yafewa abokan hamayyarsa na siyasa, da kuma afuwar da tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari ya yi wa marigayi shugaban Biafra, Chukwuemeka Odumegwu-Ojukwu, a shekarar 1982.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu: Sowore ya sanar da majalisa hanyar mika mulki ga Shettima

A cewar Onoh, irin waɗannan matakai sun nuna cewa shugabanci na siyasa zai iya amfani da tausayi da sulhu wajen warkar da rarrabuwar kawuna.

Ya yi nuni da Kundin Tsarin Mulki

Onoh ya kuma yi nuni da Sashe na 174 da 175 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, yana mai cewa sun tanadi wasu hanyoyin da za a iya amfani da su wajen magance shari’o’i.

Sashe na 174 ya bai wa Antoni-Janar na Tarayya ikon dakatar da shari’ar laifi kafin a yanke hukunci, bisa wasu sharudda da suka haɗa da maslahar jama’a da kuma muradun adalci.

Sashe na 175 kuma ya tanadi ikon shugaban ƙasa na yin afuwa a wasu yanayi da kundin tsarin mulki ya ƙayyade.

Onoh ya ce sa hannun Tinubu a lamarin El-Rufai ba zai zama alamar rauni ba, sai dai ya kasance abin da ke nuna kishin ƙasa da kwarewar siyasa.

An roki Tinubu kan El-Rufai
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

El-Rufai ya rubuta wasika

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nasir El-Rufai, ya yi magana kan shiru da wasu daga cikin tsofafin abokansa, abokan aikinsa da abokan hulɗarsa suka yi a lokacin da yake fuskantar matsaloli.

El-Rufai ya bayyana cewa bai kullaci wadanda suka zabi kin cewa komai kan halin da yake ciki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng