Duk da Sulhun da Gwamna Ya Yi, Fulani Sun Bi Dare Sun Yi Wa Mutane Kisan Rashin Imani

Duk da Sulhun da Gwamna Ya Yi, Fulani Sun Bi Dare Sun Yi Wa Mutane Kisan Rashin Imani

  • An kashe mutane shida a wani sabon hari da ake zargin wasu Fulani sun kai wa al’ummar garin Kammuku da ke Tasha-Rimi a jihar Neja
  • Magajin Garin ya ce maharan sun kai harin ne da daddare tare da kashe Musa Bahago, ɗansa Hamisu Musa da wasu bayin Sllah
  • Harin ya zo ne watanni uku bayan rikicin Kammuku da Fulani kan gonaki da hanyoyin kiwo da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 20

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa wani sabon hari da aka kai wa al’ummar kauyen Kammuku da ke Tasha-Rimi, a ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja, ya yi sanadin mutuwar mutane shida.

Bayanai sun nuna cewa an zargin wasu Fulani ne suka shiga garin dauke da makamai, suka yi wa mutane shida kisan rashin imani.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 61, an ceto shugaban ƙaramar hukumar da ya fada tarkon yan bindiga

Niger.
Taswirar jihar Neja da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Binciken da jaridar Leadership ta yi ya nuna cewa an kai harin ne da daddare, inda aka kashe mutane shida a cikin al’ummar Kammuku, lamarin da ys ksra tada hankulan jama'a.

Fulani sun kashe mutum 6 a Neja

Da yake tabbatar da lamarin ga manema labarai, magajin garin ƙauyen Tasha-Rimi, Alhaji Garba Mohammed Bissalla, ya ce mutane shida ne suka mutu a harin.

Ya bayyana cewa mutanen sun rasa rayukansu ne lokacin da wasu Fulani suka kai hari kan Musa Bahago, ɗansa Hamisu Musa da wasu mutane da daddare.

“Fulani ne suka kashe mutane shida bayan sun kai wa Musa Bahago, ɗansa Hamisu Musa da wasu hari da daddare,” in ji Bissalla.

Yadda mutane suka yi mamakin harin

Ya ce al’ummar yankin ta yi mamakin harin, musamman ganin cewa mazauna yankin sun bi umarnin gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago.

Y ce sun bi umarnin mai girma gwamna na ƙarfafa mutanensu su rungumi zaman lafiya bayan rikice-rikicen baya-bayan nan da suka faru tsakaninsu da Fulani.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

“Mun yi mamakin harin saboda mun bi umarnin gwamnan muncewa mu ƙarfafa mutanenmu su rungumi zaman lafiya bayan rikicin baya-bayan nan da ya faru da Fulani,” in ji shi.

Legit.ng Hausa ta gano cewa kimanin watanni uku da suka gabata, an samu rikici tsakanin mazauna Kammuku da Fulani a yankin Rafi kan gonaki da hanyoyin kiwo.

Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a gidan gwamnati da ke Minna Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Bayanai sun nuka cewa a yayin wannan rigima da aka yi, akalla mutane 20 suka rasa rayukansu, lamarin da ya sa gwamnatin Neja ta dhiga tsakani kuma ta sasanta su.

Sai dai wannan harim da ake zargin Fulani sun kai ya ba mzauna Kammuku mamaki duba da kokarin da aka yi na tabbatar da zaman lafiya.

Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya

A wani labarin, kun ji cewa mutane uku sun jikkata yayin da wani rikicin ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Kataeregi da ke jihar Neja a Arewacin Najeriya.

Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kwantar da tarzomar tare da tabbatar da tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262