Wata Sabuwa: Ministan Tsaro Ya Yi Zarge Zarge kan El Rufa'i da ke Tsare

Wata Sabuwa: Ministan Tsaro Ya Yi Zarge Zarge kan El Rufa'i da ke Tsare

  • Ministan tsaro, Christopher Musa, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da aikata abubuwa marasa kyau da suka haifar da rarrabuwa a jihar
  • Ya yi zargin cewa El-Rufa'i ya raba jihar gida biyu ta hanyar manufofinsa, wanda hakan ya sa mutane ba sa iya zama da juna a Kudanci da Arewacin Kaduna
  • Ministan ya yi waɗannan kalamai ne yayin da El-Rufa'i ke tsare, inda kuma ya yaba wa gwamna Uba Sani kan ƙoƙarinsa na haɗa kan mutanen jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ministan tsaro, Christopher Musa, ya fito fili ya zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da aikata abubuwa marasa kyau wadanda suka haifar da rabuwar kai mai tsanani a tsakanin al'umar jihar.

Musa ya bayyana cewa gwamnan ya jefa jihar a halin rashin haɗin kai, inda al'umma suka gaza samun 'yancin zama a tsakanin shiyyar Kudanci da Arewacin jihar sakamakon manufofinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tona gaskiya, an ji yadda gwamnoni suka amfana da cire tallafin fetur

Nasir El-Rufa'i da Christopher Musaa
Nasir El-Rufa'i a hagu da Christopher Musa a dama. Hoto: Bello El-Rufa'i|Gen CG Musa
Source: Facebook

Legit ta gano cewa ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da aka yi da shi a shirin gidan talabijin na Channels TV.

Zargin Chiris Musa ga El-Rufa'i

Musa ya bayyana damuwarsa kan yadda aka gudanar da lamura a baya, inda ya nuna cewa abin da ya faru a jihar Kaduna bai dace da ƙasa da ke da buƙatar haɗin kai ba.

Ya ce:

"El-Rufai ya aikata abubuwa masu ban tsoro a jihar Kaduna. Ya raba jihar gida biyu, ta yadda idan ka fito daga Kudancin jihar ba za ka iya komawa Arewaci ka zauna ba.
"Su ma wadanda ke Arewacin jihar suna komawa Kudanci ne. Abin da ya faru bai kamata ya kasance a garin da ke neman hadin kai ba."

Ministan ya yabi Uba Sani

Ministan ya ci gaba da cewa sabon gwamnan jihar, Uba Sani, yana yin ƙoƙari sosai wajen shawo kan wannan matsala da maido da haɗin kai tsakanin al'umma a cikin shekara ɗaya kacal da hawansa mulki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun addabi Kano, Abba ya fadi matakan da za a dauka a murkushe su

The Cable ta rahoto ya ce:

"Yanzu kowa yana da 'yancin faɗar albarkacin bakinsa. Ko da yake ba a samu komai ɗari bisa ɗari ba, amma za ka iya ganin ƙoƙarin da gwamna yake yi wajen haɗa kan mutane."
Nasir El-Rufa'i a kotu
Lokacin da za a kai Nasiru El-Rufa'i kotu. Hoto: Uche Diala
Source: Facebook

Hakazalika, ya zargi El-Rufai da rushe gidajen mutane saboda samun sabani na kashin kai tare da nuna halin ko-o-ho ko kan kashe-kashen da aka yi a Kudancin Kaduna.

Kiran SCSN kan El-Rufa'i

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar shari'a ta SCSN ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su sake duba batun ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Majalisar ta gargaɗi cewa matakan da ake gani a matsayin na siyasa ko ba tare da bin ka'ida ba na iya ruguza amincin jama'a ga cibiyoyin dimokuraɗiyya.

SCSN ta jaddada cewa tana tsaye ne kan tabbatar da adalci da tsarin doka, tare da bayyana cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙin samun kariya a ƙarƙashin doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng