Ministan Tinubu Ya Yi Magana kan Kara Albashin Ma'aikatan Najeriya

Ministan Tinubu Ya Yi Magana kan Kara Albashin Ma'aikatan Najeriya

  • Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce mafi ƙaranci albashi na N70,000 bai dace da halin matsin tattalin arzikin da ma’aikata ke fuskanta ba
  • Keyamo ya ce akwai bukatar a sake duba albashin ma’aikata zuwa sama domin rage tasirin matsin tattalin arziki da kuma ƙara ƙwazo wajen gudanar da ayyuka
  • Ministan ya kuma yi kira da a ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikata, yana mai cewa su ne ginshiƙin samar da ci gaba da tafiyar da tattalin arzikin kowace ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce albashin N70,000 ba zai wadatar ba a yanzu sakamakon matsin tattalin arzikin da ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Keyamo, wanda lauya ne mai matsayi na Babban Lauya na Ƙasa, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin taron ƙasa na 2026 kan shirye-shiryen ma’aikata kafin ritaya da XEM Consultants Limited ta shirya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sauya dabara, ta cafke kasurgumin jagoran 'yan ta'adda

Festus Keyamo a wajen taro
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo. Hoto: Festus Keyamo
Source: Facebook

Keyamo: "N70,000 ta yi kadan"

Daily Trust ta wallafa cewa Keyamo ya ce albashin da ake biya yanzu bai isa ya shawo kan girgizar tattalin arzikin da ke addabar ma’aikata ba, yana mai kira da a gaggauta ƙara albashi.

Ministan, wanda ya taɓa zama ƙaramin Ministan Ƙwadago da Ayyuka a zamanin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ya kamata gwamnati ta yi la’akari da jin daɗin ma’aikata wajen tsara manufofinta.

Ya tuna cewa yana cikin masu shiga tattaunawar da ta kai ga ƙarin mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 da ake biya a yanzu.

'Yan kungiyar kwadago
Shugabannin NLC tare da Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Bayani kan neman mafita

Keyamo ya ce akwai bukatar a sake ƙara mafi ƙarancin albashi, ko da kuwa adadin da ma’aikata ke nema ba za a iya cimma shi gaba ɗaya ba.

Ya ce gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago ya kamata su nemo matsaya ta tsaka tsakiya domin tabbatar da cewa albashin da ake biya ya yi daidai da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

Punch ta rahoto ministan ya ce idan ba a kula da ma’aikata ba, tattalin arziki ba zai iya tafiya yadda ya kamata ba, saboda aikin ɗan Adam shi ne ginshiƙin samar da ayyuka da ci gaba a ko ina a duniya.

Ana shirye-shiryen sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta fara shawarwari a matakin farkio kan sake tattauna sabon mafi ƙarancin albashi domin rage matsin tattalin arzikin da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙwadago da Ayyuka ta Tarayya, Dakta Kamil Shoretire, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron horaswa da aka shirya wa manema labaran ƙwadago.

Shoretire ya ce har yanzu gwamnati ba ta fitar da jadawalin tattaunawar a hukumance ba, amma tuni aka fara tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki, kuma za a bayyana cikakkun bayanai idan lokacin ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng