Shugaba Tinubu Ya Shilla Kasashen Waje bayan Fara Yakin Neman Zaben 2027

Shugaba Tinubu Ya Shilla Kasashen Waje bayan Fara Yakin Neman Zaben 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa Turai domin fara hutun makonni uku na shekara
  • Birnin London da ke kasar Birtaniya ne zangon farko na hutun shugaban kasar wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben 2027
  • Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan hutun domin shiga yakin neman zaben shugaban kasa na Janairu 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara hutun makonni uku a nahiyar Turai.

Shugaba Bola Tinubu ya tafi hutun ne a matsayin wani bangare na hutun shekara-shekara da yake da hakki a kai.

Shugaba Tinubu ya tafi hutu
Shugaba Bola Tinubu yana dawo hannu daga jirgin sama Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026 a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Shugabannin kwamitin yakin zabe da aka yi kafin Abdulaziz Yari daga 1999 zuwa 2027

Birnin London ne zangon farko

A cewar Bayo Onanuga, Shugaba Bola Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Turai a ranar Lahadi domin fara hutunsa na tsawon makonni uku.

“Shugaba Tinubu zai bar Abuja yau domin domin zuwa nahiyar Turai domin fara hutun makonni uku a bangaren hutunsa na shekara."

- Bayo Onanuga

Ya ce zangon farko na shugaban kasar zai kasance a London, Birtaniya, inda zai fara hutun aiki.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta ce hutun na daga cikin hutun shekara-shekara na shugaban kasa.

Zai dawo domin yakin neman zabe

Onanuga ya bayyana cewa ana sa ran Tinubu zai koma Najeriya bayan kammala hutun domin shiga harkokin yakin neman zaben shugaban kasa na Janairu 2027.

“Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo gida bayan kammala hutun domin shiga babban aikin yakin neman zabe a zaben watan Janairun 2027."

- Bayo Onanuga

Yakin neman zaben na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu ke kara shirin tunkarar babban zaben da ake sa ran zai kasance mai tsauri.

Kara karanta wannan

"Me ka ke nufi?" Fadar shugaban ƙasa ta maida martani ga Atiku kan buɗe iyakokin Najeriya

Tinubu na neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban Najeriya, yayin da ‘yan takara daga jam’iyyun adawa ke kokarin hada karfi domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.

Shugaba Tinubu ya bar Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sauran manyan 'yan takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 sun hada da Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC, Peter Obi na jam'iyyar NDC da Omoyele Sowore na jam'iyyar AAC.

Tuni dai 'yan takarar suka fara yakin neman zabe bayan hukumar INEC ta bayar da damar yin hakan. Wasu daga cikinsu har sun fara yi wa 'yan Najeriya alkawuran abubuwan da za su yi wa 'yan Najeriya.

Tinubu ya shigar da kara a Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka domin ƙalubalantar yunƙurin fitar da bayanan da suka shafi zarge-zargen da ake yi masa na safarar miyagun ƙwayoyi.

Shugaba Tinubu na ƙalubalantar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, FBI da DEA kan sakin bayanan da wani mai fafutukar ganin an samu gaskiya, Aaron Greenspan, ya nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng