Gwamnatin Tinubu Ta Sake Tsokano Atiku da Ta Ce Ta Raba wa Talakawa N600bn
- Atiku Abubakar ya ga kuskure a kalaman gwamnati ganin da farko an ce an taimakawa gidaje miliyan 15 da kudi
- Ya nuna rashin amincewa da yadda adadin iyalan da aka ce an taimaka masu ya ragu daga miliyan 15 zuwa miliyan 10
- Jigon adawar ya fi so gwamnati ta samar da tsarin rage tsada da farashin man fetur maimakon ba mutane kudi a hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Atiku Abubakar wanda yake takarar shugaban kasa a ADC ya kalubalanci lissafin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta yi ikirarin ta raba Naira biliyan 600 ga talakawa miliyan 10, batun da Atiku Abubakar yake ganin da alamar tambaya.

Source: Facebook
Tafka da warwara a maganganun gwamnatin Tinubu?
A jiya Phrank Shaibu ya fitar da jawabi a X (Twitter) a madadin Atiku Abubakar yana zargin gwamnati da yin maganganu masu cin karo da juna.
Atiku yake cewa gwamnatin APC ta taba cewa ta tallafawa gidajen marasa karfi miliyan 15 daga baya kuma ta canza alkaluma zuwa kasa da haka.
Kwanan nan sai aka ji gwamnatin tarayya tana cewa ta bada tallafin N600bn ga gidaje sama da miliyan 10.
A jawabin da hadimin na Atiku ya fitar a yammacin Alhamis, ya nuna akwai gyara a maganganun Ministan bada agaji, Dr. Bernard Doro.
Vanguard ta ce ya nemi jin ina mutane kusan miliyan biyar suka shige daga ranar 16 ga watan Yuli 2026 zuwa 26 ga watan Agusta 2026.
Ya ce:
"Wadannan ba alkaluman ‘yan adawa ba ne. Lambobin Tinubu ne masu cin karo da lambobinsa."
Atiku Abubakar ya hada gwamnati da aiki
Rahoton ya ce Atiku Abubakar ya bukaci gwamnati ta fito da cikakken bayanin gidajen da aka raba wa kudi da kuma yadda aka yi kason jiha-jiha.
Babban ‘dan adawan yana kuma so a yi bincike mai zaman kan shi domin ganin yadda aka kashe N600bn a kan mutane marasa karfi a kasar.
“Idan da gaske an kashe N600bn, sai gwamnati ta nuna inda kudin suka bi; tabatattun gidaje, kason kudin, rabon da aka yi jiha-jiha, da kudin da ba su tafi ba, wadanda suka dawo da kuma bincike mai zaman kan shi.”
- Atiku Abubakar
Atiku ya ce Tinubu ya jefa mutane a wahala
Bayan nan ‘dan siyasar ya zargi gwamnatin APC da kara jefa gidaje cikin kangin talauci a yau.
Ya ce tsare-tsaren da aka kawo sun sa fetur ya kara tsada, kudin sufuri ya tashi, farashin abinci ya yi sama kuma magunguna sun yi kudi.
Ya yi alkawarin kawo karshen tsadar rayuwa a gwamnatinsa maimakon ya rika rabon kudi sakamakon ha’ula’in da jama’a suka shiga.
Atiku ya kara da cewa:
"Idan gwamnatin Tinubu ba ta daidaita alkaluman nan ba, ta fitar da tabataccen bayanin biyan kudi, ‘yan Najeriya za su cigaba da tambaya ina gidaje miliyan biyar suka shiga?
"Sun fita daga talauci ne, suka bace daga cikin rajistar talakawa ko kuwa sun yi batan dabo ne saboda karyar gwamnati ta fi gaskiya murya?"
Atiku ya fada wa gwamnati ta bincike shi
Kun ji labari Atiku Abubakar ya bukaci Gwamnatin Najeriya ta bincike shi kan zargin cin $16bn, kuma ta gurfanar da shi idan har tana da kwararan hujjoji.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana cewa gwamnatin na amfani da tsofaffin zarge-zarge ne kawai domin janye hankalin 'yan Najeriya daga barnar su.
Idan ana da hujjar ya saci kuɗin wutar lantarki ko ya ci kudi da aka saida kadarorin gwamnati a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, bai so a raga masa.
Asali: Legit.ng


