Tafiye-Tafiye 20 a Watanni 12: Kasashen da Tinubu Ya Kai Ziyara Daga Zama Shugaban Kasa

Tafiye-Tafiye 20 a Watanni 12: Kasashen da Tinubu Ya Kai Ziyara Daga Zama Shugaban Kasa

  • A karshe dai shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya shafe makonni biyu a kasar Turai da Asiya, lamarin da ya jawo cece-kuce
  • Ziyarar da Tinubu ya kai Riyadh ta kasance ta 20, kuma Saudiyya ita ce kasa ta 14 da ya ziyara tun bayan zama shugaban Najeriya
  • A wannan rahoton, mun tattara maku dukkanin bayanan da ya kamata ku sani game da kasashen da Tinubu ya ziyarta da dalilin zuwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - A karshe dai shugaba Bola Tinubu ya koma kan karagar mulki a fadarsa da ke Abuja bayan ya shafe makonni biyu a kasashen waje.

Mai ba shugaban kasa Tinubu shawara na musamman kan bayanai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanar da dawowar shugaban a shafinsa na X.

Tinubu ya ziyarci kasashe 14 a cikin watanni 12
Shugaban Bola Tinubu ya yi tafiye-tafiye 20 a cikin watanni 12, kuma ya ziyarci kasashe 14. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Tafiye-tafiye nawa Tinubu yayi a shekara 1?

Kara karanta wannan

Naira ta koma gidan jiya, kudin Najeriya ya dawo mafi rashin daraja a duniya

Tafiyar karshe da Tinubu ya yi ita ce wadda ya halarci taron tattalin arzikin duniya tare da neman hadin gwiwar kasashe da kuma bunkasa makamashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da wannan taron ne a a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya, a ranakun Asabar da Lahadi, 28 da 29 ga Afrilu.

Dawowarsa gida a ranar Laraba 8 ga watan Mayu, ya kai ga ba da jimillar tafiye-tafiye 20 zuwa kasashen waje tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.

Haka kuma, ya kwashe kwanaki 96 a kasar waje yayin da ya yi wadannan tafiye-tafiyen.

Kasashe nawa Tinubu ya ziyarta?

Ga jerin kowace kasa da shugaban ya ziyarta tun bayan rantsar da shi da abin da ya je yi.

1. Taron yarjejeniya ta kudi a Faransa

A matsayinsa na shugaban Najeriya, kasa ta farko da Tinubu ya fara ziryata ita ce kasar Faransa, inda ya halarci taron sabuwar yarjejeniya ta kudi ta duniya.

Kara karanta wannan

"Sun lalata komai": Tsohon shugaban kasa ya koka yadda aka ruguza ayyukansa

Tafiyar dai ta faru ne bayan wata guda da rantsar da shi, kuma an ce ya yi amfani da wannan taron wajen tattaunawa da shugabannin kasashen duniya kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

2. Ziyarar kai-da-kai zuwa London

A ranar 24 ga watan Yuni, 2023, bayan kammala ziyarar da ya kai Paris, ya tashi daga Faransa zuwa London don “ziyarar kai-da-kai.”

"Tinubu, wanda aka shirya tun farko zai dawo Abuja ranar Asabar, yanzu zai wuce birnin Landan na kasar Birtaniya, domin wata gajeriyar ziyarar kai-da-kai.”

- A cewar sanarwar Dele Alake.

3. Taron ECOWAS na 63 a Guinea-Bissau (sau biyu)

A ranar 8 ga Yuli, bayan wata daya a kan mulki, Shugaba Tinubu ya ziyarci Guinea Bissau, inda ya halarci zaman taro na 63 na hukumar gudanarwar kungiyar ECOWAS.

A wajen taron ne shugabannin kasashen yankin suka zabi Tinubu a matsayin shugaban kungiyar kasashen yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Tinubu ya kai ziyara ta biyu zuwa Guinea-Bissau a ranar 16 ga Nuwambar 2023, inda ya halarci bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai.

4. Taron kungiyar Tarayyar Afirka a Kenya

A ranar Asabar, 15 ga watan Yuli, kasar Kenya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da shugaban Najeriya ya kai ziyara cikin kwanaki 100 na farko a kan karagar mulki.

Ziyarar ta kasance taron kungiyar Tarayyar Afirka (AU) na farko da Tinubu ya halarta a matsayin shugaban Najeriya.

5. Taron bikin dimokuradiyyar Jamhuriyar Benin

A ranar Talata, 1 ga watan Agustar 2023, shugaba Tinubu ya ziyarci jamhuriyar Benin tare da gwamnoni shida domin murnar dimokuradiyyar kasar.

Shugaban ya yi wannan tafiyar ne a lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta sanar da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Harajin CBN: Na hannun daman Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi

6. Taron kugniyar G20 a Indiya

A ranar 5 ga watan Satumbar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya isa New Delhi, babban birnin Indiya a ziyarar aiki ta kwanaki shida, inda ya halarci taron kolin shugabannin kasashen G20.

Shugaban ya je Indiya tare da wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministoci da mataimakan shugaban kasa.

7. Taron UN karo na 78 a Amurka

A ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya isa Amurka inda ya halarci manyan tarukan da aka gudanar a yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

An ruwaito cewa akalla shugabannin duniya 145 ne suke halartar wannan taron na diflomasiyya, wanda ake tattauna batutuwan da suka shafi tattali, tsaro, yanayi da sauransu.

8. Ganawa da Sarkin UAE, da taron COP28 a Abu Dhabi da Dubai

A ranar 11 ga watan Satumba, 2023, Mohammed bin Zayed Al Nahyan, shugaban dadaddiyar daular Larabawa (UAE), ya karbi bakuncin Shugaba Bola Tinubu a Abu Dhabi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi watsa watsa da Gwamnatin Bola Tinubu saboda lafta harajin 0.5% a banki

A karshen ganawar da shugabannin biyu suka yi, hadaddiyar daular Larabawa ta janye haramcin biza da ta kakaba wa matafiya na Najeriya.

A ranar 29 ga watan Nuwambar 2023 kuwa, Tinubu ya ya tashi daga Abuja zuwa Dubai, hadaddiyar daular Larabawa inda ya halarci taron COP28 na canjin yanayi.

9. Taron G20 (CWA) a Jamus

A ranar 19 ga watan Nuwambar 2024, Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Berlin na kasar Jamus inda ya halarci taron G20 Compact with Africa (CWA).

Taron na G20 CWA ya gudana ne tare da taron zuba jari na G20 karo na hudu, wanda gwamnatin Jamus da kungiyoyin kasuwanci na Jamus suka shirya.

10. Taron kungiyar AU na 37 a Ethiopia

A ranar 15 ga watan Fabrairu, Shugaba Bola Tinubu ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha domin halartar babban taron kungiyar AU karo na 37.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tafiyar Tinubu da aka ce ya 'ɓata' kafin ya dawo

Shugaban ya bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka wajen gudanar da manyan tarurruka kan sauye-sauyen hukumomin Tarayyar Afirka; zaman lafiya da tsaro da kuma sauyin yanayi.

11. Ziyarar aiki a kasar Qatar

A ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2024, Shugaba Bola Tinubu ya bar jihar Legas zuwa Doha na kasar Qatar a wata ziyarar aiki.

Shugaban kasa, Tinubu ya amsa gayyatar mai martaba, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, Sarkin Qatar, inda aka shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniya da suka shafi tattalin arziki.

12. Taron rantsar da shugaban kasa a Senegal

A ranar Talata 2 ga Afrilu, 2024, Shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa Dakar, Senegal, domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.

Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ya bi sahun sauran shugabannin yankin da suka halarci bikin rantsuwar a cibiyar baje koli ta Diamniadio.

Kara karanta wannan

Wa ke jagorantar Najeriya yanzu? Atiku ya tambaya yayin da Shettima ya tafi Amurka

13. Taron kasuwanci dazuba jari a Netherlands

A ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, shugaba Tinubu ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Hague, Netherlands inda ya halarci taron kasuwanci da zuba jari na Najeriya da Netherland.

Ya yi amfani da wannan damar wajen karfafa dangantakar tattalin arziki da diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.

14. Taron WEF a kasar Saudiya

A ranar 27 ga watan Afrilu, 2024, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya inda ya halarci taron tattalin arziki (WEF) kan hadin gwiwar duniya, da kuma makamashi.

Shugaba Tinubu da mukarrabansa sun yi amfani da damar taron WEF domin tattauna da shugabannin duniya kan batutuwan suka shafi tsare-tsaren Tinubu na ajandar 'Renewed Hope'.

Tinubu ya ba Oba Sikiru lambar GCON

A wani rahoton, mun ruwaito maku cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba sarkin kasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona lambar girmamawa ta 'Grand Commander of Order of Nigeria'.

Tinubu wanda ya samu wakilcin Kashim Shettima, ya kuma taya basaraken murnar cika shekara 90 a duniya tare da bayyana shi a matsayin gwarzon dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.