An Yi Abin Kirki: Jami'an 'Yan Sanda Sun Ceto 'Yan Bautar Kasa 11 a Hannun 'Yan Bindiga
- Jami'an 'yan sanda a jihar Kogi sun samu nasarar ceto mutane 11 da 'yan ta'adda suka sace a hanyar Kogi
- Daga cikin wadanda aka ceton har da 'yan bautar kasa da aka sace da direbobinsu, lamarin da ya tada kura
- Wasu 'yan uwan wadanda lamarin ya shafa sun yi ikirarin cewa har yanzu 'yan uwansu ba su tsira daga hannun 'yan ta'addan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lokoja, Jihar Kogi - Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi ta samu nasarar ceto mutane 11 da 'yan ta'adda saka yi awon gaba da su, ciki har da 'yan bautar kasa (NYSC) da direbobi guda biyu.
Lamarin ya auku ne a ranar Laraba a hanyar Aloma-Egane a karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi. Mutanen na kan hanyarsu ne komawa gida daga sansanin horar da mambobin NYSC da ke karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, Saliu Afusat, ta tabbatar da gudanar da aikin ceton a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, rahoton The Cable.

Source: Original
Wadanda aka ceto
Afusat ta bayyana cewa jami'an tsaro sun kai dauki cikin hanzari inda suka ceto mutane 11 daga hannun tsagerun. Ta kara da cewa yawancin wadanda aka ceton mambobin NYSC ne da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Abuja.
A cewar sanarwar, miyagun 'yan bindiga ne suka fito daga daji kusa da mahadar Ogene Zaria da Onicha-Igo da misalin karfe 4:40 na yamma, inda suka tare motoci biyu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji.
Shugaban 'yan sanda na yankin Ofu ya jagoranci jami'an tsaro zuwa inda abin ya faru. A wurin ne aka samu motoci biyu da aka bar su, guda daya kirar Hummer da kuma wata motar bas mai kujerum 18.
Bayan gudanar da bincike a daji, an samu nasarar ceto mutane 11. Hukumar ta tantace su tare da ba su damar ci gaba da tafiya bayan kammala binciken farko.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da cewa tana amfani da dukkan kayan aiki da dabarun tsaro domin gano sauran mutanen da ke hannun tsagerun.
Yan uwa sun magantu a shafukan sada zumunta
Wannan lamari ya tayar da hankula a dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), inda 'yan uwan wadanda aka sace suka bayyana cewa har yanzu 'yan uwansu ba su samu 'yanci ba.
A wani bidiyo da ya yadu, wata budurwa mai suna Chidimma ta bayyana cikin kuka tana rokon gwamnati da hukumar NYSC da su shigo cikin al'amarin domin ceto yar uwarta.
Chidimma ta bayyana cewa yar uwarta ta gama samun horo na sati uku a Bayelsa kuma aka tura ta jihar Niger, inda ta tsara kwana a Abuja kafin ta wuce wurin aikinta.
Ta ce a kan hanyarsu ta zuwa Abuja ne aka kai musu hari, aka kashe direba sannan aka tafi da 'yan bautar kasar cikin daji.
An roki NYSC da gwamnati su ceto wadanda aka sace
Wani mutum mai suna Chisom Ede shi ma ya wallafa cewa 'yar uwarsa tana cikin wadanda aka sace a kan hanyar ta Kogi. Ya roki hukumar NYSC, gwamnatin tarayya da jami'an tsaro da su dauki matakin gaggawa domin ceto su.
Haka zalika, wani mai amfani da dandalin X mai suna @ddevilsworkshop ya bayyana cewa 'yar uwarsa tana cikin wadanda abin ya shafa.
Ya kuma yada jerin sunayen mutanen da ke cikin motar Peace Mass Transit tare da bayyana cewa masu garkuwar suna neman kudin fansa har Naira miliyan 20.
Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


