Gobara Ta Babbaka Uwa da 'Ya'yanta 4, Sun Mutu cikin ban Tausayi

Gobara Ta Babbaka Uwa da 'Ya'yanta 4, Sun Mutu cikin ban Tausayi

  • Wata mata da ’ya’yanta hudu sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a gidansu da ke yankin Okochiri a Jihar Rivers
  • An rahoto cewa lamarin ya faru ne a safiyar Juma’a, inda gobarar ta lakume gidan tare da kona mutanen biyar har lahira
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da mutuwar matar da ’ya’yanta, yayin da wasu mutanen da ke cikin gidan suka samu raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Port Harcourt – Wata mata da ’ya’yanta hudu sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a gidansu da ke Okochiri, karamar hukumar Okrika a Jihar Rivers.

Lamarin ya faru ne a safiyar Juma’a, inda aka gano gawarwakin matar da ’ya’yanta bayan jami’an da suka isa wurin sun tarar da gidan ya kone.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Jami'an hukumar kashe gobara
Ma'aikatan kashe gobara a Najeriya. Hoto: Federal Fire Service
Source: Twitter

Uwa da ’ya’yanta sun mutu

Punch ta wallafa cewa jami'an tsaro na karamar hukumar Okrika, Igwe Godswill, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa cikakken bayani kan musabbabin gobarar bai samu ba tukuna.

Godswill ya ce lokacin da shi da tawagarsa suka isa wurin, sun tarar da gawarwakin matar da ’ya’yanta hudu.

Ya ce jami’an ’yan sanda sun riga sun isa wurin domin tattara bayanan abin da ya faru.

Wani da ya san abin da ya faru, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce gobarar ta tashi ne lokacin da wani mutum ke kokarin zuba man fetur a cikin jarka.

A cewarsa, man fetur din ya kama wuta a lokacin da ake kokarin zuba shi, lamarin da ya haddasa gobarar.

’Yan sanda sun fara bincike

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Rivers, Blessing Agabe, ta tabbatar da faruwar gobarar.

Sai dai Agabe ta ce matar da ’ya’yanta uku ne suka mutu, yayin da wasu mutanen da ke cikin gidan suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Gwamnan Najeriya da ke biyan ma'aikatan shi N500,000 a wata

Rahoton Channesl TV ya nuna cewa ta ce dukiya da aka kiyasta darajarta da dubban Naira ta lalace sakamakon gobarar.

Agabe ta ce an fara bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa gobarar da kuma sauran abubuwan da suka kai ga faruwar lamarin.

Taswirar jihar Rivers
Taswirar jihar Rivers a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Gidan ya kone kurmus

Godswill ya ce matasan yankin sun riga sun kashe gobarar kafin shi da tawagarsa su isa wurin.

Rahotanni sun nuna cewa ya ce ana kyautata zaton mutanen sun mutu ne kafin a samu nasarar kashe wutar.

Bidiyon da aka gani daga wurin ya nuna wata mata tana korafi kan ginin gidan, wanda gobarar ta lalata rufinsa da wasu sassan gidan sosai.

An yi gobara a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa wata gobara ta tashi a wani bangare na gidan Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ke yankin GRA na Gusau, babban birnin jihar.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 7:20 na dare, lamarin da ya sa aka tura jami’an kashe gobara zuwa gidan domin dakile wutar.

A lokacin da ake kokarin kashe gobarar, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara ta ce tana aiki domin shawo kan lamarin, yayin da ba a bayyana musabbabin gobarar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng