Ana So Hukuma Ta Kama Ciyaman Din da zai Kori 'Yan Garinsa da ba Su APC

Ana So Hukuma Ta Kama Ciyaman Din da zai Kori 'Yan Garinsa da ba Su APC

  • Jam'iyyar ADC ta bukaci jami'an tsaro su gaggauta kama shugaban karamar hukumar Kuje, Danjuma Shekwolo, tare da gurfanar da shi a kotu
  • ADC ta ce kalaman Shekwolo na cewa wadanda ba za su goyi bayan APC ba su bar Kuje barazana ce ga hakkokin 'yan kasa da kundin tsarin mulki ya tanada
  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ma ta bukaci a dauki mataki kan shugaban, tana mai cewa barazanar siyasa ta saba da doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta kama shugaban karamar hukumar Kuje da ke Abuja, Danjuma Shekwolo, bisa wasu kalamai da ya yi kan masu adawa da jam'iyyar APC.

ADC ta bayyana cewa kalaman Shekwolo na cewa mazauna Kuje su goyi bayan APC ko su bar yankin barazana ce ga hakkokin 'yan kasa da kuma wani yunkurin tilasta masu sauya matsayarsu ta siyasa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace matar sarki, sun hau TikTok sun nemi a aiko masu N20m

Samuel Danjuma Shekwolo
Ciyaman din Kuje, Samuel Danjuma Shekwolo. Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa jam'iyyar adawar ta bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu, da hukumar DSS su kama Shekwolo tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Ana son kama ciyamin din Kuje

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi ya fitar ranar Laraba, ADC ta bayyana kalaman shugaban Kuje a matsayin "barazanar tilasta korar jama'a daga muhallinsu."

Shekwolo ya ce ba zai amince da adawar wasu mazauna yankin ba, yana mai cewa sun ci moriyar ayyukan gwamnatin shugaba Bola Tinubu da kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Jam'iyyar ADC ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ba 'yan kasa damar shiga jam'iyyar siyasa da suke so, zama a duk inda suka ga dama a kasar da kuma kare su daga wariya saboda ra'ayinsu na siyasa.

Ta ce sashe na 40, 41 da 42 na kundin tsarin mulkin kasa sun tabbatar da wadannan hakkoki, saboda haka bai kamata wani shugaban siyasa ya tilasta wa jama'a goyon bayan wata jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, an sace matar hakimi da likita a Kaduna

Kungiyar Amnesty ta yi martani

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce mazauna Kuje za su ci gaba da rayuwa cikin fargaba matukar hukumomin tsaro ba su dauki mataki kan barazanar da shugaban karamar hukumar ya yi ba.

Kungiyar ta wallafa a X cewa ta ce yunkurin sanya goyon bayan APC a matsayin sharadin rayuwa cikin kwanciyar hankali da gudanar da hakkokin dan kasa a Kuje abu ne da ya sabawa doka.

Tunji Disu a bakin aiki
Sufeto janar na 'yan sanda, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

APC ta shirya zaben 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da sake bude rajistar mambobinta ta hanyar intanet a fadin Najeriya daga ranar 31 ga watan Agustan 2026.

Jam'iyyar ta ce za a gudanar da rajistar a dukkan gundumomi, inda tsofaffin mambobi za su tabbatar da bayanansu yayin da sababbin masu shiga za su samu damar yin rajista.

Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka, ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen jam'iyyar na karfafa tsarinta da kuma gina ingantaccen kundin bayanan mambobi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng