Bayan Shekaru 53, Tinubu Ya Amince da Canza Fasalin Aikin Bautar Kasa na NYSC a Najeriya

Bayan Shekaru 53, Tinubu Ya Amince da Canza Fasalin Aikin Bautar Kasa na NYSC a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta amince da yi wa hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) garambawul bayan shekaru 53 da kafa ta
  • Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa
  • Olawande ya bayyana cewa garambawul ɗin zai bai wa gwamnati damar tantance manufofi da tsarin gudanar da hukumr NYSC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta amince da gudanar da garambawul ga tsarin Hukumar Kula da Matasa 'Yan Bautar Ƙasa (NYSC).

Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja yau Litinin, 29 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Olawande ya bayyana cewa an amince da sake fasalin NYSC ne a taron majalisar zartarwa da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tinubu ya amince da gyara shirin NYSC

A cewarsa, garambawul ɗin zai haɗa da cikakken nazari kan yadda shirin NYSC ke gudana domin ya dace da bukatun Najeriya na yanzu.

Bayanai sun nuna cewa an kafa shirin NYSC ne a shekarar 1973 domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa bayan yaƙin basasa da Najeriya ta fuskanta.

Tsawon shekaru 53, shirin ya kasance wata hanya ta haɗa sababbin daliban da suka kammala jami'a daga sassa daban-daban na ƙasar tare da bunƙasa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al'umma.

Dalilin yi wa NYSC garambawul

Sai dai ministan ya ce bayan shafe shekaru da dama ana gudanar da shirin, ya zama wajibi a sake duba tsarin saboda sauye-sauyen da suka faru a ƙasar.

Kara karanta wannan

Abin da sabuwar dokar kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya ta kunsa

A rahoton da Vanguard ta wallafa, Olawande ya ce:

"Bukatun ƙasarmu sun sauya, kuma mutane da dama suna sa ran manufofin NYSC su ma su sauya domin su dace da halin da ake ciki a yanzu."
NYSC.
Matasa masu yiwa kasa hidima suna daukr horo a sansanin NYSC Hoto: @NYSC_ng
Source: Facebook

Za a sake duba manufofin NYSC

Olawande ya bayyana cewa garambawul ɗin zai bai wa gwamnati damar tantance ko manufofi da tsarin gudanar da NYSC har yanzu suna biyan bukatun ƙasa.

Sai dai bai bayyana cikakken bayani kan sauye-sauyen da za a aiwatar ko lokacin da za a fara aiwatar da garambawul ɗin ba.

Za a fara biyan 'yan NYSC alawus a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da fara biyan alawus da tallafin kudi ga masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ak turo a jihar.

Gwamna Lawal ya bayar da umarni ga Ofishin Akanta Janar da ya yi dukkan shirye-shiryen da suka dace domin aiwatar da wannan shiri na bai wa masu yi wa kasa hidima alawus.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi magana kan kashe malamar Islamiyya a Kaduna

A cewar gwamnatin Zamfara, wannan mataki na nuna irin jajircewar Gwamna Lawal wajen kula da walwala da jin dadin matasan da ke bayar da gudunmawa wajen bunkasa jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262