Sanata Yari Ya Bayyana Mutanen da Za Su Taka Muhimmiyar Rawa a Tazarcen Tinubu

Sanata Yari Ya Bayyana Mutanen da Za Su Taka Muhimmiyar Rawa a Tazarcen Tinubu

  • Abdulaziz Yari ya ce matasan Najeriya na daga cikin manyan ƙungiyoyin da APC ke buƙata domin yaɗa manufofin gwamnatin Tinubu
  • Yari ya ce matasa za su yi amfani da kafafen sada zumunta da hanyoyin hulɗar al’umma wajen bayyana ayyukan gwamnatin Tinubu
  • Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na shirin ƙaddamar da tsarin wayar da kan matasa a faɗin ƙasar gabanin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Daraktan-Janar na kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, ya ce matasan Najeriya za su kasance masu matuƙar muhimmanci wajen isar da sakonnin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Yari ya ce matasa za su taka muhimmiyar rawa wajen isar da manufofi da abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cimma a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda zuwa ga al’umma.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗauki zafi, Bola Tinubu ya shiga ganawa da gwamnonin APC a Aso Rock

Sanata Yari ya yi magana kan kamfen din Tinubu
Sanata Abdulaziz Yari tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Matasa za su yaɗa sakon gwamnati

Jaridar Leadership ta ce Yari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 lokacin da ya karɓi Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Tinubu kuma mai rajin ƙarfafa matasa, wanda ya kai masa ziyara domin taya shi murnar samun muƙamin.

Yari ya ce matasan Najeriya ba makomar ƙasa kawai ba ne, illa kuma wani muhimmin ginshiƙi ne a harkokin siyasa da zamantakewar ƙasar a yanzu.

“Matasa ba makomar wannan ƙasa kawai ba ne, su ne yanzu. Idan za mu bayyana gaskiyar abin da wannan gwamnati ta cimma, daga ababen more rayuwa zuwa tattalin arziki da tsaro, matasanmu ne za su yaɗa wannan saƙo cikin sauri da gamsarwa,” in ji shi.

Ya ce matasa sun fi samun damar isar da saƙonnin siyasa saboda ƙwarewarsu wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani.

APC na son matasa su zama jakadu

Sanata Yari ya ce tattaunawarsa da Seyi Tinubu ta fi mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma gina ingantaccen tsarin tattara matasa domin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

Ya bayyana Seyi Tinubu a matsayin wanda ya nuna himma wajen tallafa wa matasa, yana mai cewa irin wannan ƙoƙari ne kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ke buƙata.

Tsohon gwamnan ya ce jam’iyyar ba za ta tsaya kawai wajen neman matasa su jefa mata ƙuri’a ba, illa tana son su taka rawa wajen bayyana manufofi da nasarorin gwamnati.

“Ba kawai muna neman matasan Najeriya su zaɓe mu ba ne, muna son su zama jakadun o Renewed Hope a cikin al’ummominsu, a yanar gizo da kuma wajen yanar gizo,” in ji Yari.

Za a kaddamar da tsarin wayar da kan matasa

Daraktan ya bayyana cewa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC na kammala wani tsari na wayar da kan matasa a faɗin Najeriya.

Yari ya ce tsarin zai yi amfani da kafafen sada zumunta, ƙungiyoyin al’umma da tsarin siyasar matakin ƙasa domin isar da bayanai kan ayyukan gwamnatin Tinubu.

Ya kuma ce shirin zai mayar da hankali wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya, ta hanyar bai wa matasa sahihan bayanai da za su iya yaɗawa a kafafen sadarwa daban-daban.

Kara karanta wannan

Kamfen ya fara daukar zafi, Peter Obi ya sake kalubalantar Tinubu

Sanata Yari ya yi magana kan Tinubu
Sanata Abdulaziz Yari zaune a ofis Hoto: Al'mansoor Gusau
Source: Facebook

Kwankwaso ya ba Sanata Yari shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki tsarin kwamitin yakin neman zaɓen APC na zaɓen 2027.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma buƙaci Abdul’aziz Yari ya sake duba matsayinsa na jagorantar yakin neman zaben Shugaba Tinubu a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng