Malaman Musulunci 500 Karkashin Sheikh Jingir Sun Goyi bayan Tazarcen Tinubu
- Malaman addinin Musulunci da shugabannin siyasa sama da 500 sun amince da sake zaben Shugaba Bola Tinubu
- An bayyana hakan ne yayin wani taron JIBWIS a Jos, inda mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Jibril Barau ya halarta
- JIBWIS ta kuma jaddada muhimmancin gaskiya, kwarewa, adalci da rikon amana, tare da yin kira da a inganta tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Ana shirin babban zaben 2027 ta bayyana a Jos, malamai Musulunci sun nuna goyon baya ga Bola Tinubu.
Taron ya samu halartar manyan yan siyasa ciki har da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Jibril Barau da gwamnoni.

Source: Facebook
Barau ya shiga cikin malaman addinin Musulunci da masu ruwa da tsaki sama da 500 wajen amincewa da Shugaba Bola Tinubu domin wa’adin mulki na biyu, cewar Arise News.

Kara karanta wannan
Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani
Malaman Izala sun mara wa Tinubu baya
An bayyana amincewar ne yayin wani taron kasa da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis-Sunnah (JIBWIS) ta shirya a Jos.
A cewar sanarwar da taron ya fitar, sama da mutane 350 ne suka halarta, ciki har da fitattun malaman addinin Musulunci da shugabannin siyasa.
Haka kuma, malamai da masana, kwararru da wakilan matasa daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarci taron da aka gudanar.
Shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ne ya jagoranci taron, wanda kuma ya samu halartar wasu manyan jami’an gwamnati.

Source: Facebook
Wadanda suka halarci taron a Jos
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnonin Kano, Sokoto, Yobe da Jigawa, da Ministan Albarkatun Ruwa da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa.
Haka kuma, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa yana daga cikin manyan jami’an da suka halarci taron na JIBWIS.
Amincewar da aka bai wa Shugaba Tinubu ta kara wa taron wani yanayi na siyasa, musamman yayin da ‘yan siyasa ke shirin babban zaben 2027.
JIBWIS ta kuma yi alkawarin goyon bayan duk wani matsayi da Shugaban Majalisar Ulama’u ta kungiyar, Sheikh Jingir, zai dauka game da zaben.
Wannan matsayi na iya hada da goyon bayan tsarin takarar shugaban kasa da mataimakinsa Musulmi, wato tikitin Musulmi da Musulmi.
Sai dai kungiyar ta jaddada cewa shigar mutane cikin siyasa ya kamata ta kasance bisa gaskiya, kwarewa, adalci, rikon amana da hidimar al’umma.
Ta ce bai kamata a mayar da siyasa kan muradun kabila ko wani bangare na kasa ba, maimakon bukatun Najeriya baki daya, cewar Punch.
Taron ya kuma bukaci jam’iyyun siyasa su karfafa dimokuradiyyar cikin gida tare da mayar da hankali kan kamfen da ya shafi manufofi da matsalolin jama’a.
Dalilin malaman Musulunci na goyon bayan Tinubu
An ji cewa sama da malaman Musulunci 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja ne suka bayyana goyon bayansu ga sake zaben Bola Tinubu a 2027.
Ministan Gidaje, Muttaka Rabe Darma ya fito ya yi karin haske kan dalilin malaman na daukar wannan mataki.
Taron malaman ya yaba da inganta tsaro a Kaduna, Katsina da Sokoto, tare da neman ƙarin aiki a Neja da Zamfara.
Asali: Legit.ng
