Hanyar Abuja: 'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi awon gaba da 16

Hanyar Abuja: 'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi awon gaba da 16

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun harbe direbobi guda biyu tare da sace fasinjoji 16 a kauyen Idu da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa karin wasu fasinjoji uku sun samu raunukan harbin bindiga, amma an garzaya da su zuwa babban asibitin tarayya (FMC) da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar Daily Trust, daya daga cikin direbobin da 'yan bindigar suka kashe sunansa Nicholas Ofodile.

Usman, wani direba da ya tsallake rijiya da baya yayin harin 'yan bindigar, ya shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:48 na safiyar ranar Laraba.

Ya ce 'yan bindigar; dauke da muggan makamai, sun bullo kwatsam daga cikin daji tare da budewa motocin matafiya wuta daga kowanne bangare na babbar hanyar mai hannu biyu.

A cewarsa, 'yan bindigar; wadanda yawansu ya haura 30, sun sauko daga kan wani tsauni da ke daura da wata kwana mai hatsari, lamarin da yasa motocin da suka shawo kwanar a guje zarcewa cikin jeji, ba tare da sanin abinda ke faruwa ba.

Ya ce direbobin da 'yan bindigar suka kashe sun yi rashin sa'a saboda motocinsu ne a kan gaba yayin da 'yan ta'addar suka bude wuta.

Hanyar Abuja: 'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi awon gaba da 16
Hanyar Abuja
Asali: Twitter

Usman ya ce fasinjojin cikin motocin ne 'yan bindigar suka yi garkuwa da su bayan sun kashe direbobinsu.

Direban ya bayyana cewa da kyar ya tsallake rijiya da baya a yayin da 'yan bindigar suka kai harin.

"Allah ne ya kubutar da ni har na tsaya daukan fasinja a hanya. Motocin direbobin da aka harbe sune a gabana, sun bani tazarar wasu kilomitoci.

DUBA WANNAN: Sanatan APC ya bukaci a mayar da aikin majalisa na wucin gadi, a rage albashin mambobi

"Nan da nan na taka birki bayan na hango abinda ke faruwa, ba tare da bata lokaci ba na juya, na koma da baya," a cewarsa.

Wani mazuaunin yankin mai suna Sulaiman ya ce tuni suka binne gawar daya daga cikin direbobin da aka harbe, yayin da aka dauki gawar Nicholas zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin Lokoja.

DSP William Aya, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai.

"Yanzun nan aka kirani tare da sanar da ni cewa an kashe mai babban shagon 'Chucks Supermarket' da wani mutum guda.

"Har yanzu rundunarmu ba ta da bayanan abinda ya faru," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel