Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Yi Wa NYSC Gyare Gyare Karon Farko cikin Shekara 53

Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Yi Wa NYSC Gyare Gyare Karon Farko cikin Shekara 53

  • Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da yi wa tsarin hukumar yi wa kasa hidima gyare-gyare a karon farko tun bayan kafuwarta
  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fito ya bayyana dalilin da ya sanya gwamnatinsa ta amince a yi gyare-gyaren
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa amincewa da gyare-gyaren na daga cikin wani bangare na alkawuran da ya daukarwa matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta amince da gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima na NYSC.

Shugaba Tinubu ya ce gyare-gyaren na da nufin wadatar da matasan Najeriya da fasahohin aikace-aikace da kuma shirya su domin ci gaban kasa.

Shugaba Tinubu ya yi magana kan NYSC
Shugaba Bola Tinubu da wasu matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) Hoto: Bayo Onanuga, National Youth Service Corps
Source: Facebook

Shugaba Tinubu a bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta mamaye yankunan Legas, hanyoyi sun yi makil, lantarki ta katse

Meyasa Tinubu ya amince da gyare-gyaren

Haka kuma shugaban kasar ya bayyana cewa gyare-gyaren, wadanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da su, na daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta dauka na samar da gamsassun damarmaki ga matasa.

“A ranar Litinin, a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya, gwamnatinmu ta amince da gyare-gayre mafi muhimmanci a tsarin hukumar yi ka kasa hidima (NYSC) tun bayan kafuwarta a shekarar 1973.”
“A ranar da aka rantsar da ni a matsayin shugabanku, na yi alkawarin samar da gamsassun damarmaki ga matasanmu. Na ce mata da matasa za su samu dama a gwamnatinmu, kuma wannan gyara na daya daga cikin tabbatar da wannan alkawari."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ce lokacin gyara ya yi a NYSC

Ya ce ko da yake NYSC ta yi aiki don tabbatar da hadin kan kasa na tsawon shekaru sama da 50, gyaren-gyaren da aka samu a halin yanzu a kasar suna bukataer sabuwar hanyar tafiyar da su.

Kara karanta wannan

Jerin gyare gyare 7 da Gwamnatin Tinubu ta yi wa NYSC a karon farko tun 1973

“Har na tsawon shekaru 53, NYSC ta yi aiki don tabbatar da hadin kan kasa. Wannan manufa tana da muhimmanci kuma dole ne a kiyaye ta."
“Amma Najeriyar yau tana bukatar fiye da haka. Matasanmu kusan kashi 70 cikin 100 ne na al'ummar mu.

- Shugaba Bola Tinubu

Za a sauya tsarin hukumar NYSC
Wasu matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) Hoto: National Youth Service Corps
Source: Facebook

Za a horar da matasa

Shugaban kasar ya ce shirin bayar da horarwa yanzu zai dauki tsawon makonni shida kuma zai mayar da hankali kan nauyin da ke wuyan dan kasa, shugabanci, dabi'u, shirye-shiryen aiki, kasuwanci, ilimin na'ura mai kwakwalwa da na kudi.

A cewarsa, za a horar da matasan a fannonin da suka hada da aikin gona, lafiya, ilimi, fasaha, shari'a, aikin gwamnati, abubuwan raya kasa, tattalin arziki, kasuwanci, tattalin arziki na fasaha da kuma ayyukan jami'an tsaro da na farin kaya.

"Dole ne kowane mai yi wa kasa hidima ya bar NYSC yana da shiri mafi kyau don aiki, kasuwanci da kuma hidimar kasa."

- Shugaba Bola Tinubu

Uba Sani ya yabawa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya

A cewar Gwamna Uba Sani, yankin Arewacin Najetiya bai taba samun ayyuka masu yawa ba kamar yadda ya samu a lokacin mulkin Tinubu.

Uba Sani ya ce hakan na bayyana ne ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa, tallafin noma da kuma inganta harkokin lafiya da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng