An Biya ‘Yan bindiga Kudi Sun Sako Yara 48 da Suka Yi Garkuwa da Su a Neja
- Yara 48 daga cikin 54 da aka sace lokacin suna girbin gyaɗa sun dawo gida da aka biya kuɗin fansa
- Ana zargin mutanen Dogo Gide suka sace yaran a karo na biyu bayan gungun farko sun sake su a jeji
- Wata yarinya guda ɗaya ta rasu a hannun ɓarayin, yayin da wasu biyar suka samu nasarar sulalewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - A halin yanzu ‘yan bindiga sun saki yara 48 da suka yi garkuwa da su can kwanakin baya a wani kauye a jihar Neja.
Yaran da suka shaki iskanci kanana ne da shekarunsa yake tsakanin bakwai zuwa 12, kuma sun shafe makonni uku a hannun miyagun.

Source: Getty Images
Wata majiya ta shaida wa AFP cewa wadannan yara sun kubuta amma sai da aka biya ‘yan bindigan kudin fansa kafin a sake su.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano
Ta'adin 'yan bindiga a Arewacin Najeriya
Wadannan gungun ‘yan bindiga sun kware wajen dauke bayin Allah, su yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa a Najeriya.
Baya ga daukar mutane domin samun kudi, sun yi suna a sace daruruwan dabbobi da kuma lafta haraji a kan manoma a cikin kauyuka.
A kan daura haraji a kan manoma kafin su yi girbi ko kuma su bukaci jama’a su tara masu kudi domin kawai su tsira daga hare-harensu.
Rahoton Daily Trust ya ce wannan ya fi kamari a yankin da ake hakar ma’adanai a Arewa.
An biya kudi an fanshi yara 48
Mai garin kauyen Mashegu, Abdullahi Sahonrami ya shaida cewa a daren shekaran jiya an saki yara 40 da aka yi garkuwa da su.
Daga baya kuma a daren jiya, ‘yan bindigan sun sake fito da ragowar yaran takwas.
A farkon watan Agustan nan ne ‘yan bindigan suka dauke yara 54 lokacin da suke girbe gyada a wata gona da ke kauyen Sabon Rijiya.
Labarin yaran da aka yi garkuwa da su
Yaran sun shafe kwanaki uku a jejin Zugurma, Abdullahi Sahonrami ya ce amma an ci sa’a domin an sake su ba tare da an biya kudi ba.
Sai dai ana cikin murna an sake su, sai yaran Dogo Gide suka yi ram da su a hanya.
Wani jami’in majalisar dinkin duniya ya shaida wa manema labarai cewa ana tunanin wannan gungu suna da alaka da sojojin Ansaru.

Source: Getty Images
Dama can akwai wata yarinya guda da ta mutu a hannun gungun farko da suka dauke su.
Da suka fada hannun ‘yan ta’addan daga baya, wasu yara biyar sun tsere, don haka ne ya zama yara 48 ne miyagun suka yi garkuwa da su.
Zancen dauke masallata a jihar Neja
Kun ji labarin fushin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna sakamakon sace masallata da 'yan bindiga suka yi a Jihar Neja kwanan nan.
Shugaban kasar ya umarci Sojoji, 'Yan sanda, hukumar DSS, da sauran hukumomin tsaro da na leken asiri da su haɗa kai a ceto su cikin gaggawa.
An kutsa masallatai huɗu a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida, da Gidan-Zana da ke ƙaramar hukumar Borgu aka dauke jama'a suna sallah.
Asali: Legit.ng
