Yan Bindiga Sun Rutsa Fitaccen Dan Kasuwa a Masallaci bayan Sallar Isha'i
- ’Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani dan kasuwa a Dabi da ke Kwali, Abuja
- An sace Alhaji Yusuf Keche ne jim kadan bayan ya idar da Sallar Isha’i a wani masallaci da ke kusa da gidansa
- Wani mazaunin yankin ya ce ’yan bindigar sun yi amfani da motar da ba ta da lamba wajen yin garkuwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani ɗan kasuwa, Alhaji Yusuf Keche.
Maharan sun sace sanannen dan kasuwar ne bayan ya idar da Sallar Isha’i a wani masallaci da ke Dabi, Karamar Hukumar Kwali da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Source: Original
Yadda aka sace dan kasuwa a Abuja
Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin Dabi, Ibrahim Suleiman, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin, jim kadan bayan ya idar da Sallar Isha’i a wani masallaci da ke kusa da gidansa.
Ya ce dan kasuwan yana kan hanyarsa ta komawa gida ne lokacin da wasu ’yan bindiga da ke dauke da bindigogin AK-47 suka tasa keyarss zuwa wurin da ba a sani ba.
A cewarsa, yan bindigar sun fito daga wata mota mai duhun gilashi wadda ba ta da lamba, suka tilasta masa shiga motar sannan suka yi awon gaba da shi yayin da suke ta harbe-harbe.
A cewar Suleiman, biyu daga cikin ’yan bindigar sun riga sun fake a kusa da masallacin kafin sauran ’yan kungiyar su fito daga motar suka tilasta wa Alhaji Yusuf shiga cikin motar da ke jiransa.
An zargin sun dade suna bibiyarsa
Ya ce yadda ’yan bindigar suka gudanar da aikin ya nuna cewa sun dade suna bibiyar motsin mutumin.
“Yadda aka gudanar da aikin a fili yake nuna cewa ’yan bindigar sun dade suna sa ido kan motsin mutumin, domin yadda suka yi aikin ya yi kama da fim,” in ji shi.
Suleiman, wanda gidansa yake kusa da masallacin, ya ce da farko ya dauka wani irin karar wutar lantarki ce ya ji, kafin daga bisani ya fahimci cewa karar harbe-harbe bindiga ne.
Wani mataunin yankin, wanda ke sana’ar sayar da kayan masarufi kusa da masallacin amma ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce nan take ya kulle kansa a cikin shagon bayan jin karar harbe-harben.

Source: Twitter
Ya ce ya fito ne bayan ’yan bindigar sun bar wurin, sannan ya rufe shagon ya koma gida, kamar yadda rahoton Punch ya kawo.
Ya kara da cewa tun kafin lamarin ya faru, ya lura da wani mai babur yana yawo cikin yanayin da ya sanya shi zargi.
Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, SP Josephine Adeh, ta ce ba ta da masaniya kan sabon lamarin garkuwar.
Yan bindiga sun sace matar Hakimi a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa masu garkuwa da mutane sun kashe wasu mazauna kauyen Abu biyu yayin da suke kokarin tserewa da likita da matar Hakimi da suka sace.
Sojojin Operation Enduring Peace sun kaddamar da farmaki da aikin ceto domin kubutar da wadanda aka sace a karamar hukumar Sanga ta Kaduna.
Asali: Legit.ng

