Yan Bindiga Sun Shiga Fadar Sarki, Sun Kashe Shi bayan Korafi kan Ayyukansu a Niger

Yan Bindiga Sun Shiga Fadar Sarki, Sun Kashe Shi bayan Korafi kan Ayyukansu a Niger

  • Wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani basarake q fadarsa bayan ya yi korafi kan ayyukansu a yankin Borgu
  • Kisan ya zo ne kwanaki biyu bayan ’yan bindigar sun hallaka mutum sama da 30 a masallaci tare da sace wasu masu ibada.
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai buƙatar jami’an tsaro su kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Borgu, Niger - Rahotanni sun ruwaito cewa wasu yan bindiga sun hallaka wani basarake a fadarsa da ke a jihar Niger.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kashewa da garkuwa da wasu masu ibada a wani masallaci, wasu ’yan bindiga da ake zargi sun kashe.

Yan bindiga sun kashe basarake a fadarsa a Niger
Marigayi Sarkin Borgu, Alhaji Ahmed Yusuf da Gwamna Umaru Mohammed Bago. Hoto: @NigerStateNG.
Source: Twitter

Gwamna Umaru Mohammed Bago ya mika saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da al’ummar Galla baki ɗaya a shafin a X.

Kara karanta wannan

Ba yadda ake tsammani ba, gwamna ya fadi silar rashin tsaro a yankinsa

Yadda ƴan bindiga suka lashe basarake a Niger

An kashe Hakimin ƙauyen Galla da ke ƙaramar hukumar Borgu, Alhaji Ahmed Yusuf, wanda rahotanni suka ce shi ne babban ɗan’uwan Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi.

An harbe shi a fadarsa ne kwanaki kaɗan bayan ya koka kan ayyukan ’yan bindiga da ake zargi suna addabar al’ummar yankin.

Wannan kisan ya faru ne kimanin sa’o’i 48 bayan ’yan bindigar sun hallaka akalla mutum 30 a cikin wani masallaci, tare da yin garkuwa da wasu mutane.

Bincike ya nuna cewa Hakimin ya kalubalanci ’yan bindigar da ake zargi da mamaye Masarautar Borgu, inda ya bukace su da su mutunta darajar rayuwar jama’a.

Ya kuma gargade su da su daina shiga yankinsa, lamarin da wakilin jaridar ya ce ’yan bindigar suka ɗauka a matsayin cin fuska.

Rahotanni sun ce wannan gargadi ne ya sa ’yan bindigar mamaye fadar Hakimin washegari, inda suka harbe shi har lahira.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata da 'yan bindiga suka sace masallata a Neja, ya bayar da umarni

A wani labarin kuma, Gwamnan Niger, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana alhininsa kan kisan Hakimin ƙauyen Galla da ke Masarautar Borgu, Alhaji Ahmed Yusuf.

Gwamna Bago ya yi jimamin mutuwar Sarki
Gwamna Umaru Mohammed Bago na jihar Niger. Hoto: Umaru Mohammed Bago.
Source: Twitter

Sakon ta'aziyyar Gwamna Bago

Gwamna Bago ya ce kashe Hakimin a fadarsa ya nuna ƙarfin hali da rashin kunya daga ’yan bindigar.

Saƙon ta’aziyyar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Bologi Ibrahim, ya sanya wa hannu, ya buƙaci jami’an tsaro su tabbatar an kama waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.

Gwamna Bago ya jajantawa Ministan, iyalan marigayin, al’ummar Galla da Masarautar Borgu baki ɗaya bisa rasuwar Hakimin.

Ya kuma buƙaci su yi haƙuri, yana mai cewa marigayin ya rayu rayuwa mai kyau, kuma ya mutu yana kare al’ummar da ke ƙarƙashin kulawarsa.

Sace masallata: Tinubu ya umarci jami'an tsaro

An ji cewa Bola Tinubu ya umarci Sojoji, ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su haɗa kai wajen ceto mutanen da aka sace a Jihar Neja.

Yan ta’adda dauke da makamai sun kutsa masallatai huɗu yayin sallar Juma’a tare da tafiya da masu ibada zuwa daji.

Shugaban ƙasa ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an dawo da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.