'Yan Bindiga Sun Samu Naira biliyan 7 na Kudin Fansa cikin Shekara 1 a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Samu Naira biliyan 7 na Kudin Fansa cikin Shekara 1 a Najeriya

  • Ƙungiyar bincike ta SBM Intelligence ta bayyana cewa an sace mutane 7,825 a Najeriya cikin shekara guda, yayin da aka kashe aƙalla mutum 1,142
  • Rahoton ya nuna cewa iyalan wadanda aka sace sun biya kusan Naira biliyan 7.8 a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa da mutane
  • Masana harkokin tsaro sun ce yawaitar biyan kudin fansa na kara karfafa masu aikata laifuka wajen sayen makamai da ci gaba da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Wani sabon rahoto da cibiyar bincike ta SBM Intelligence ta fitar ya bayyana yadda satar mutane domin neman kudin fansa ke kara zama babbar hanyar samun kudi ga masu aikata laifuffuka a Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa an sace aƙalla mutane 7,825 a cikin hare-haren satar mutane 1,713 tsakanin watan Yuli na 2025 zuwa Yunin 2026.

Kara karanta wannan

An shiga yanayin tashin hankali da bam ya tashi da mutane a jihar Zamfara

Yan bindiga masu garkuwa da mutane
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa iyalan wadanda aka sace sun biya kusan Naira biliyan 7.8 a matsayin kudin fansa cikin wannan lokaci.

Nawa aka biya masu garkuwa?

SBM Intelligence ta bayyana cewa kudin da masu garkuwa da mutane suka nema ya ragu daga Naira biliyan 48 zuwa Naira biliyan 22.9.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ainihin kudin da aka biya ya karu daga Naira biliyan 2.56 zuwa kusan Naira biliyan 7.78.

Hakan ya nuna cewa yawan kudin da masu garkuwa suka samu daga wadanda suka nema ya karu daga kashi 5.35 zuwa kashi 34 cikin 100.

Rahoton ya ce kusan kashi 90 cikin 100 na kudin fansar da aka biya ya shiga hannun wata kungiyar Boko Haram mai suna Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal-Jihad.

A cewar rahoton da Business Day ta wallafa, kungiyar ta samu kusan Naira biliyan 7 daga hare-haren satar mutane guda takwas kacal.

Kara karanta wannan

An biya ‘yan bindiga kudi sun sako yara 48 da suka yi garkuwa da su a Neja

Hare-haren da aka kai a Najeriya

Rahoton ya ce manyan hare-haren satar mutane masu yawa sun zama daya daga cikin hanyoyin da masu aikata laifuka suka fi amfani da su.

An ce satar mutane 416 a Ngoshe da ke jihar Borno ta kai ga biyan kusan Naira biliyan 5 a matsayin fansa.

Haka kuma, an ce an biya kusan Naira biliyan 2 domin sakin dalibai da ma'aikata 315 na makarantar St Mary's School da ke Papiri a jihar Neja.

Wasu 'yan bindiga a Katsina
Ado Aliero da wasu 'yan bindiga a wajen sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Jihar Zamfara ce ta fi samun yawan manyan hare-haren satar mutane, inda aka samu irin wannan hari sau 92.

Rahoton ya ce jihar Sokoto ma ta samu hare-haren satar mutane masu yawa guda 76 a cikin lokacin da aka gudanar da binciken.

SBM Intelligence ta ce sake yawaitar satar dalibai na iya yin mummunar illa ga ilimi, noma da kuma amincewar jama'a da hukumomin tsaro.

An kama dan kungiyar ISWAP

Kara karanta wannan

Trump ya shiga matukar damuwa bayan rasuwar mawakiyar Amurka, Parton

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar jami'an CJTF sun kama wani mutum da ake zargi da alaka da kungiyar ISWAP a jihar Borno.

An kama mutumin mai suna Buba Hammadu, mai shekaru 25, a garin Mairari da ke karamar hukumar Guzamala bayan jami'an tsaro sun gudanar da wani samame a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa bayan kama shi, jami'an tsaro sun gano wata hotuna a wayarsa tare da wasu mutane dauke da bindigogin AK-47, lamarin da ya kara jefa shakku kan alakarsa da kungiyar ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng