Trump Ya Shiga Matukar Damuwa bayan Rasuwar Mawakiyar Amurka, Parton

Trump Ya Shiga Matukar Damuwa bayan Rasuwar Mawakiyar Amurka, Parton

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin sauke tutocin kasar kasa domin girmama fitacciyar mawakiya Dolly Parton bayan rasuwarta
  • Trump ya bayyana rasuwar Parton mai shekaru 80 a matsayin babban rashi ga miliyoyin mutane, yana mai yabawa da irin gudunmawar da ta bayar
  • Rahotannin da Leigit Hausa ta samu sun nuna cewa an ce za a sauke tutocin daga karfe 6:00 na yammacin ranar Talata har tsawon mako guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin sauke tutocin kasar domin girmama fitacciyar mawakiyar kasar kuma 'yar wasan kwaikwayo, Dolly Parton, wacce ta rasu tana da shekaru 80.

Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa, inda ya bayyana Parton a matsayin daya daga cikin manyan mawakan duniya ta taba gani.

Kara karanta wannan

An taso gwamnoni a gaba bayan FAAC ta cika aljihunsu da N47tr

Mawakiyar Amurka, Dolly Parton
Dolly Parton da ta rasu a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Politico ta rahoto ya ce rasuwar mawakiyar babban rashi ne ga miliyoyin mutane, yana mai cewa babu kamarta kuma ba za a sake samun irinta ba.

Gudunmawar Parton a Amurka

Shugaban Amurkan ya kara da cewa za a fara sauke tutocin kasar daga karfe 6:00 na yammacin ranar Talata, inda za su ci gaba da kasancewa a rabin sanda har tsawon mako guda.

Donald Trump ta kuma yi mata addu'ar samun salama, yana mai cewa duniya tana kaunarta saboda irin tasirin da ta yi a rayuwar mutane.

Iyalan Dolly Parton sun sanar da rasuwarta ta hanyar wani faifan bidiyo da suka wallafa a shafukan sada zumunta, sai dai ba su bayyana musabbabin mutuwarta ba.

Ana yi jimamin rasuwar Parton

Bayan sanar da rasuwarta, 'yan siyasa daga jam'iyyun Republican da Democrat sun bayyana alhininsu tare da yabawa da irin tasirin da Dolly Parton ta yi a fannin waka da ayyukan jin kai.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano

Parton ta yi kaurin suna wajen taimakon al'umma, musamman ta hanyar shirin Imagination Library da ta kafa a shekarar 1995, wanda ke raba littattafai kyauta ga jarirai da kananan yara.

An ruwaito cewa shirin ya raba littattafai sama da miliyan 200 ga yara, lamarin da ya sa ake yabawa da irin gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen inganta ilimi.

New York Times ta wallafa cewa a halin yanzu dai 'yan uwa da abokan arziki na cigaba da jimamin rasuwar mawakiyar a ciki da wajen kasar Amurka.

Trump ya sa dokar biza

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta dakatar da ba masu shiga da fita biza a Amurka daga kowace kasa a duniya.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Trump ta dakatar da karbar wasu bukatun takardun izinin shiga Amurka na masu neman zama a kasar daga sassa daban-daban na duniya, a wani mataki na kara tsaurara dokokin shige da fice.

An bayyana cewa za a dawo cigaba da aiki bayan jami'an Amurka sun samu cikakkiyar kwarewa a wani horo na musamman da aka shirya masu saboda kakkabe bakin da bai kamata su shiga kasar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng