An Samu Hotunan 'Yan Ta'adda da Makamai a Wayar Wanda Sojoji Suka Kama
- Sojojin Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar CJTF sun cafke wani matashi da ake zargi da alaka da kungiyar ISWAP a jihar Borno
- Jami'an tsaro sun gano wani hoto a wayarsa da ya nuna shi tare da wasu mutane dauke da bindigogin AK-47, lamarin da ya kara jefa shi cikin zargi
- An mika wanda ake zargin zuwa hedikwatar Sashen 3 na Operation Hadin Kai domin ci gaba da bincike da daukar matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar jami'an CJTF, sun cafke wani mutum mai shekaru 25 da ake zargi da kasancewa mamba ko kuma yana da alaka da kungiyar ISWAP.
An cafke mutumin mai suna Buba Hammadu ne a garin Mairari da ke karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano

Source: Facebook
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa sojojin FOB, Mairari ne suka gudanar da aikin tare da hadin gwiwar dakarun CJTF.
Abin da jami'an tsaro suka gano
Bayan cafke Hammadu, jami'an tsaro sun gudanar da binciken farko a kansa domin gano ko akwai wata alaka tsakaninsa da 'yan ta'adda da ke gudanar da ayyuka a yankin.

Source: Original
A yayin binciken, an gano wani hoto a wayarsa da ya nuna wanda ake zargin tare da wasu mutane da ba a bayyana sunayensu ba, yayin da suke rike da bindigogin AK-47.
Rahoton ya ce gano hoton ya kara jefa Buba Hammadu cikin zargin yiwuwar kasancewarsa ko kuma samun alaka da mayakan ISWAP da ke aiki a yankin tafkin Chadi.
Kayayyakin da aka kwato a hannunsa
Daga cikin kayayyakin da jami'an tsaro suka samu daga hannun wanda ake zargin akwai wayar Tecno guda daya, laima, kibiya, carbi, madubi da kuma maganin ciwon ido.
Daga bisani, an mika Buba Hammadu zuwa hannun Hedikwatar Sashen 3 na Operation Hadin Kai domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Rahoton ya ce kama shi wani bangare ne na ci gaba da ayyukan tsaro da suka dogara da bayanan sirri, domin ganowa tare da tarwatsa hanyoyin sadarwa da masu taimaka wa kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin tafkin Chadi.
Amurka ta horas na sojojin Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Amurka sun fara horas da dakarun Najeriya kan amfani da jirage marasa matuka da sauran dabarun aikin soja domin kara karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.
An gudanar da horon ne a wani sansanin aiki da ke jihar Bauchi, a karkashin wani babban shirin hadin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.
Rahoton rundunar AFRICOM ta Amurka ya ce horon ya hada da koyar da dabarun ceto da jinyar wadanda suka ji raunuka a fagen fama, amfani da makamai, dabarun boye kai, tace ruwa da gwajinsa, kawar da abubuwa masu fashewa da sauransu.
Asali: Legit.ng
