Sojoji Sun Rutsa Yan Ta'adda Masu Karɓar Kudin Fansa a Jihar Kebbi

Sojoji Sun Rutsa Yan Ta'adda Masu Karɓar Kudin Fansa a Jihar Kebbi

  • Sojojin Operation Fansan Yamma sun kubutar da wata mata da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da ita a jihar Kebbi a yayin da aka yi aikin ceto
  • Jami'an sojoji sun tarwatsa shirin karɓar kuɗin fansa, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tsere wa tare da barin matar a wurin
  • Rundunar ta ce za ta ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga lamba, tare da kira ga jama’a su rika ba jami’an tsaro sahihan bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Sojojin Sector 2 na Operation Fansan Yamma sun kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita, tare da dakile wani shirin karɓar kuɗin fansa a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata da 'yan bindiga suka sace masallata a Neja, ya bayar da umarni

Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan rundunar ta samu sahihin bayanin sirri kan shirin biyan kuɗin fansar matar da aka sace daga gonarta a watan da ya gabata.

Yan ta'adda sun gamu da gamonsu a jihar Kebbi
Wasu daga cikin dakarun sojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na cikin wata da Osoba ya fitar, inda ya jami'an na samun bayanai, suka gaggauta gaggauta tunkarar wurin domin dakile musayar kuɗin.

An kori yan ta'adda a Kebbi

Daily Post ra ruwaito Osaba ya ce ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin tunkarar sojojin bayan sun hango su, amma ƙarfin makaman sojojin ya tilasta musu tserewa cikin rudani, inda suka bar matar a baya.

A kalamansa:

“Arangamar ta tilasta wa ’yan ta’addan tserewa cikin rudani, inda suka bar matar da aka yi garkuwa da ita, wadda daga baya sojojinmu suka samu nasarar kubutar da ita."

Ya ƙara da cewa an samu matar ba tare da wata illa ba, sannan sojojin suka kai ta cikin aminci domin ta koma wajen iyalanta a Danko-Wasagu.

An ceto wata mata a jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi mai fama da matsalar rashin tsaro Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Bayan kubutar da matar, sojoji sun gudanar da cikakken bincike a hanyar da ’yan ta’addan suka bi wajen tserewa, domin tabbatar da cewa an tabbatar da tsaron yankin gaba ɗaya kafin su koma sansaninsu lafiya."

Kara karanta wannan

Bayan gargadin DSS, sojoji sun rika aman wuta a kan yan bindiga a Sokoto

Sojoji sun sha alawashi kan yan ta'adda

A wani aiki makamancin haka, Osoba ya ce sojojin sun gudanar da sintiri na yau da kullum da kuma aikin tabbatar da iko a wasu sassan ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar.

Ya ce an kammala aikin ba tare da samun wata matsala ba, yana mai bayyana shi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin rundunar na hana miyagu samun damar zirga-zirga cikin ’yanci a yankin.

Kakakin rundunar ya tabbatar wa mazauna Kebbi cewa Operation Fansan Yamma za ta ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga lamba a jihar da sauran sassan Najeriya.

Yan taadda sun hallaka yan sanda a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Zamfara ta ce ta kashe ’yan bindiga 17 bayan jami’an tsaro sun yi musayar wuta da su a kokarin dakile hari.

’Yan bindigar sun kai hari kan motocin kasuwanci biyu, inda suka kashe direbobi da fasinjoji bakwai, suka raunata wasu da jefa jamaa a cikin firgici da neman tsira.

Rundunar ta ce jami’an tsaro sun kaddamar da samame kan maboyar ’yan bindigar, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng