An Taso Gwamnoni a gaba bayan FAAC Ta Cika Aljihunsu da N47tr
- Gwamnonin jihohin Najeriya 36 na fuskantar matsin lamba kan yadda suka kashe kudaden da suka samu daga asusun tarayya a cikin shekaru uku
- Najeriya ta raba kusan N47.25tn ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi tsakanin 2023 da 2025, fiye da rabin jimillar kudaden da aka raba a baya
- Masana sun ce karuwar kudaden shiga bai inganta rayuwar ’yan Najeriya yadda ya kamata ba, yayin da tsadar rayuwa, rashin aikin yi ke yawaita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya na fuskantar karin tambayoyi kan yadda suka kashe makudan kudaden da suka samu daga asusun FAAC a cikin shekaru uku da suka gabata.
Wannan na zuwa ne bayan bayyanar bayanai da suka ce FAAC ta raba kusan N47tn ga matakan gwamnati uku tun bayan cire tallafin man fetur.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa bayanan da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta fitar sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya, jihohi 36 da kananan hukumomi 774 sun samu jimillar N93.216tn daga FAAC tsakanin shekarar 2017 zuwa 2025.
Gwamnatoci sun samu karin kudi daga FAAC
Rahoton ya kara da cewa sai dai fiye da rabin wannan kudi, wato N47.25tn, an raba shi ne tsakanin 2023 zuwa 2025 kadai a tsakanin rukunin gwamnatocin uku.
Wannan ya nuna gagarumin karuwar kudaden shiga bayan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta bullo da su a shekarar 2023.

Source: Facebook
Daga cikn wadannan sauye-sauye da suka kawi karuwar kudin akwai cire tallafin man fetur, gyaran tsarin musayar kudaden waje da kuma kara kokarin tattara kudaden shiga.
Duk da haka, masana tattalin arziki da manufofin gwamnati, kungiyoyin fararen hula da sauran masu sharhi na cewa karuwar kudaden shiga ba ta haifar da daidaitaccen sauyi a rayuwar ’yan Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Masani ya magantu kan karin kudin gwamnatoci
Wani masani kan manufofin gwamnati, Adebayo Abubakar, ya ce cire tallafin man fetur ya taimaka wajen kara kudaden shiga na gwamnati.
Ya kara da bayyana cewa amma ba a mayar da karin kudaden gaba daya zuwa ayyukan da suka dace da halin da ’yan Najeriya ke ciki ba.
A kalamansa:
“Hanyoyi, gadoji, magudanan ruwa da sauran ababen more rayuwa na da matukar muhimmanci, amma wasu gwamnatoci sun fi karkata ne ga manyan ayyuka da ake iya gani, yayin da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, samar da ruwa da sauran muhimman ayyuka ke samun karancin kulawa."
Bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa kudaden FAAC da ake rabawa sun tashi daga N5.64tn a shekarar 2017 zuwa N21.90tn a 2025, abin da ke nuna karuwar kusan kashi 288 cikin 100 cikin shekaru tara.
A shekarar 2017 an raba N5.64tn, yayin da aka raba N7.98tn a 2018. A 2019 kuma kudaden sun ragu zuwa N7.85tn, sannan suka kara faduwa zuwa N7.11tn a 2020.

Kara karanta wannan
Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa
FAAC ta raba wa gwamnatoci kudi
A baya, kun ji cewa Kwamitin raba kudin asusun tarayya (FAAC) ya ce gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi (LGAs) sun raba jimillar N3.007tn a watan Yulin 2027.
Adadin shi ne mafi girman rabon kuɗin da aka samu zuwa yanzu tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki. A watan Yuni, FAAC ta raba N2.5tn ga matakan gwamnati.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bawa Mokwa, daraktan hulɗa da jama’a a ofishin babban akawun tarayya, ya fitar ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026.
Asali: Legit.ng
