'Yan Uwan Dan Shagamu da Aka Kashe a Kano Sun Bayyana Wani Sirri kafin Mutuwarsa
- Yan uwan Ibrahim Khalil Dan Shagamu sun bayyana cewa marigayin ya riƙa tsoron rayuwarsa, har ya daina kwana a gidansa saboda zargin barazana
- ’Yar uwarsa ta ce wasu mutane sun taɓa ƙoƙarin su yaudare shi domin ya fito daga gida, suna iƙirarin za su ba shi tallafin gwamnati
- Dan Shagamu ya taɓa wallafa bidiyoyi yana zargin wasu matasa da yi masa barazana, jifa a gidansa da lalata wasu kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Yan uwan marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu, mai sharhin siyasa na Kano, sun bayyana cewa ya riƙa nuna fargabar za a iya kashe shi kafin a gano gawarsa a gidansa.
An gano Dan Shagamu a mace a gidansa da ke Gaida, ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano, ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026.

Source: Twitter
Ya daina kwana a gidansa saboda tsoro
Da take magana da ’yan jarida ranar Laraba, ’yar uwar marigayin mai suna Halima, ta ce ɗan uwanta ya daina kwana a gidansa saboda yana ganin rayuwarsa na cikin haɗari, cewar rahoton Vanguard.
Ta ce Dan Shagamu ya sha bayyana mata cewa wasu mutane na neman su cutar da shi, lamarin da ya sa ya koma kwana a wajen wani abokinsa.
“Ya yi zargin cewa wasu mutane suna neman ransa, don haka ya daina kwana a gida. Ya zauna da wani abokinsa kuma ya guji duk inda yake jin akwai barazana,” in ji ta.
Halima ta kuma tuna wani lokaci da wasu mutane suka yi ƙoƙarin yaudarar ɗan uwanta domin ya fito daga gidansa.
A cewarta, mutanen sun ce suna son ba shi tallafin kayan agaji daga gwamnatin tarayya, amma ya fara zarginsu bayan sun umurce shi da zuwa wani wuri domin karɓar lambar da za ta ba shi damar samun tallafin.
Abokinsa ya sanar da ’yan sanda
Halima ta ce fargabar su game da inda Dan Shagamu yake ta ƙaru ne bayan abokinsa ya riƙa zuwa gidansa ya same shi a kulle.
Daga bisani, abokin nasa ya tuntubi ’yan sanda domin neman taimako. Ɗan uwan marigayin, Muhammad Hizbullah Kabiru, ya ce daga baya wasu ’yan uwa suka shiga gidan tare da jami’an ’yan sanda, inda suka tarar da shi ya mutu.
Ya bayyana cewa yanayin da suka tarar da gawar ya nuna cewa marigayin ya samu munanan raunuka.
Ya taɓa zargin matasa da yi masa barazana
Kafin mutuwarsa, Dan Shagamu ya wallafa wasu bidiyoyi a kafafen sada zumunta, inda ya yi zargin cewa wasu matasa da ke unguwarsu sun yi masa barazana.
A wani bidiyon, ya ce matsalar ta fara ne bayan wasu yara sun nemi ya ba su sadaka, amma ya gaya musu cewa a lokacin ba shi da abin da zai ba su.

Kara karanta wannan
Da gaske Akpabio ya yi wa 'yan Arewa barazanar shan azaba idan Tinubu ya fadi a 2027?
Ya ce daga baya lamarin ya ƙara tsananta, inda wasu matasan suka yi masa barazana tare da jifan gidansa da duwatsu. A cewarsa, jifan ya yi sanadin lalacewar wasu kayayyaki a gidansa.
Ya nemi taimakon ’yan sanda da Sarkin Kano
Dan Shagamu ya kuma yi zargin cewa wasu iyaye da shugabannin al’umma sun kasa shiga tsakani duk da korafe-korafen da ya gabatar musu.
Saboda haka, ya ce ya nemi taimakon ’yan sanda da kuma Sarkin Kano domin samun kariya da magance matsalar.
A halin yanzu, ’yan sanda na ci gaba da bincike kan mutuwar Dan Shagamu, yayin da iyalansa ke jiran gano ainihin abin da ya faru da shi.

Source: Original
Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan Dan Shagamu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar damuwarsa kan kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu.
Kwankwaso ya buƙaci hukumomin Kano su gudanar da bincike cikin tsanaki domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Asali: Legit.ng

