EFCC Ta Cika Umarnin Tinubu, An Bude Asusun Gwamnatin Osun
- Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, EFCC ta cire matakin hana cire kudi daga asusun gwamnatin Osun da ta daskarar a baya
- EFCC ta ce ta fara binciken yadda aka sarrafa N11bn na kudaden muhalli da tallafi tun daga watan Maris, 2026 inda ta garkame asusun daga baya
- Wani babban mataimaki ga Tinubu ya tabbatar da cewa an bude asusun bayan umarnin shugaban kasar na cewa gaskiya an ba shi kunya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta cire matakin hana cire kudi daga asusun gwamnatin jihar Osun, bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar da ta bude asusun.
Rahotanni sun tabbatar da cewa asusun gwamnatin jihar da ke ajiye a bankunan First Bank of Nigeria da Zenith Bank yanzu sun fara aiki.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa EFCC ta sanya dokar Post No Debit kan asusun gwamnatin jihar a ranar 5 ga Agusta, 2026 tana mai cewa tana binciken zargin karkatar da kudaden jama'a.
Binciken EFCC ya jawo cece-kuce
Premium Times ta wallafa cewa hukumar ta ce tana binciken yadda aka sarrafa kusan N11bn da suka hada da kudaden muhalli, kudaden tallafi da kuma kudaden rabon gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Matakin ya jawo suka daga bangarori daban-daban, inda wasu suka zargi EFCC da amfani da binciken a matsayin matakin siyasa domin raunana Gwamna Ademola Adeleke gabanin zaben da aka kammala.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matakin EFCC a matsayin abin kunya, sannan ya umarci hukumar da ta cire dokar da ta hana amfani da asusun.
EFCC ta bi umarnin Tinubu
Bayan an ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben, ya umarci Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'a na jihar, Oluwole Jimi-Bada, SAN, da ya janye karar da aka shigar kan EFCC.

Kara karanta wannan
Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa
Sai dai Temitope Ajayi, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Yada Labarai da Hulda da Jama'a, ya tabbatar da cewa an bude asusun.
Ya ce:
“An cire dokar. EFCC ba za ta iya yin watsi da umarnin shugaban kasa ba. Zan iya tabbatar maka cewa an yi hakan nan take,"
Wani hadimin Gwamna Adeleke, wanda ya nemi a sakaya sunansa, shi ma ya tabbatar da cewa an cire dokar hana cire kudi daga asusun.
Tinubu ya gana da shugaban EFCC
A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya gana da shugaban EFCC da ministan gidaje kan hanyar da sarrafa da sayar da gidajen da aka kwace daga wadanda ake zargi da almundahana.
Ganawar ta zo ne kwanaki uku bayan Ademola Adeleke ya sake lashe zaben gwamnan Osun da kuma janye karar da jihar ta shigar kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Shugaban kasa Tinubu ya taba umartar EFCC da ta janye umarnin da ta samu na daskarar da asusun gwamnatin Osun lamarin da ya jawo maganganu kan yancin hukumar na yin aiki kai tsaye.
Asali: Legit.ng
