An Gano Manyan Hadurra 3 da Ke cikin Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

An Gano Manyan Hadurra 3 da Ke cikin Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Fetur

  • Fadar shugaban kasa ta soki shirin Atiku na dawo da tallafin mai, tana mai cewa zai magance alamomin matsala ne kawai ba tushenta ba
  • Sunday Dare ya ce sayar da danyen mai ga matatun cikin gida kan farashin rangwame zai rage kudaden shiga ga gwamnatin tarayya
  • Fadar shugaban kasa ta yi gargadin cewa manufar na iya dawo da fasa-kwaurin man fetur da kuma dagula kasuwar man Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da shirin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress (ADC) a 2027, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur.

Fadar ta bayyana shirin a matsayin wata manufar tattalin arziki da za ta magance alamomin matsala na dan lokaci, maimakon magance tushen matsalolin da ke addabar bangaren makamashi na Najeriya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya saba da Atiku, ya bayyana babbar matsalar dawo da tallafin fetur

An soki Atiku kan shirin dawo da tallafi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Sunday Dare, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwar jama’a ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026.

Ya bayyana matsayar gwamnatin ne bayan Atiku ya sake jaddada kudirinsa na sayar da danyen man Najeriya ga matatun cikin gida kan farashi na musamman domin rage kudin man fetur ga ‘yan kasa.

Waye zai biya kudin tallafin?

Dare ya ce sayar da danyen man da ke karkashin ikon tarayya kasa da farashin kasuwa zai haifar da gibi nan take a kudaden da ke shiga asusun gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa kudaden da a kullum za su shiga asusun tarayya domin rabawa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi za su ragu.

A cewarsa, hakan na iya shafar kudaden da ake amfani da su wajen samar da makarantu, asibitoci da tsaro.

Dare ya bayyana shirin a matsayin wani gibi na kasafin kudi da aka lullube shi da sunan manufar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya bayyana 'barayin' da yake fafatawa da su a zaben 2027

Shirin zai dagula kasuwar mai

Fadar Shugaban Kasa ta kuma nuna damuwa kan illar da irin wannan tsari zai iya haifarwa ga tsarin kasuwar man fetur a Najeriya.

Dare ya ce bai wa wasu matatun mai danyen mai kan farashi na musamman na iya samar da wata fa’ida ta wucin gadi ga wasu kamfanoni, lamarin da ka iya jefa kananan matatun mai na ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ya kuma ce manufar na iya sabawa tsarin bude kasuwar man fetur ga gasa da Dokar Masana’antar Man Fetur (Petroleum Industry Act) ta tanada.

A cewarsa, dokar ta samar da tsarin da zai karfafa gasa a bangaren makamashi, maimakon gwamnati ta ci gaba da sanya farashi ko bayar da wasu fifiko na musamman.

Matsalar dawowar fasa-kwauri

Wani babban abin da Fadar Shugaban Kasa ta damu da shi shi ne yiwuwar dawo da fasa-kwaurin man fetur zuwa kasashe makwabta.

Sunday Dare ya ce idan aka samar da babban gibi tsakanin farashin man fetur a Najeriya da farashin man a kasashen makwabta na Yammacin Afirka, hakan zai kara karfin gwiwar masu safarar man fetur ta haramtacciyar hanya.

Kara karanta wannan

Atiku ya fito ya yi bidiyo kan dawo da tallafin mai da aka fara yada jita jita

Ya ce tarihi ya nuna cewa idan aka samu man fetur mai rahusa a Najeriya fiye da kasashen makwabta, masu fasa-kwauri kan yi amfani da wannan damar domin samun riba.

A cewarsa, ko da Atiku ya yi alkawarin samar da tsauraran hanyoyin sa ido da tantancewa, karfin ribar da ake samu daga safarar man da aka yi wa tallafi na iya sa a yi watsi da irin wadannan matakan.

Wace shawara Sunday Dare ya bayar?

Dare ya kammala da cewa shirin dawo da tallafin man fetur zai iya samar da sauki na gajeren lokaci, amma ba zai magance manyan matsalolin da ke cikin tsarin makamashi na Najeriya ba.

Ya kwatanta manufar da yin amfani da maganin rage radadi wajen magance ciwo mai tsanani, yana mai cewa hakan na iya rage radadin na dan lokaci amma ya bar ainihin matsalar ba tare da an magance ta ba.

Fadar Shugaban Kasa ta ce ya kamata a mayar da hankali wajen samar da ingantaccen tsarin makamashi mai dorewa, karfafa matatun mai na cikin gida da kuma samar da kasuwar da za ta yi aiki bisa ka’idojin gasa.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Gwamnatin Tinubu ta soki shirin Atiku
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sowore zai dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zabe a 2027

Omoyele Sowore ya ce cire tallafin ya ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng