Gwamna Abba Ya Ruguza Lissafin Kwankwaso da Sauran Iyayen Gida a Siyasar Kano
- Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Abdulmalik Suleiman, ya ce salon Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya yanayin siyasar Kano
- Suleiman ya ce sauya sheƙar Abba zuwa APC ta taimaka wajen haɗa manyan shugabannin siyasa, wanda hakan ya raunata siyasar ubangida
- Ya ce haɗin kan shugabannin APC a Kano ya ƙara wa jam’iyyar ƙarfi gabanin babban zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Abdulmalik Suleiman, ya ce salon siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ayyukan raya ƙasa sun sauya yanayin siyasar Kano.
Suleiman ya bayyana haka ne a Kano ranar Talata yayin da yake tsokaci kan sabon sauyin kawance a siyasar jihar Kano.

Source: Facebook
Ya ce Abba Kabir ya rage tasirin siyasar ubangids, wacce ta shahara a Kano ta hanyar gina nasa matsayar siyasa da kuma kulla alaƙa da manyan ’yan siyasa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Sauya shekar Abba ya canza Kano
A cewarsa, sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar APC mai mulki ta kuma taimaka wajen haɗa manyan shugabanni da tsofaffin gwamnoni, ciki har da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau da Sanata Kabir Gaya.
Abdulmalik Suleiman ya ce:
“Gwamna Abba mutum ne mai iya tafiyar da mutane. Tun bayan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ya iya haɗa kan dukkan shugabanni da tsofaffin gwamnoni, Ganduje, Shekarau da Sanata Kabir Gaya.
Ya ce sulhun da aka samu ya warware wasu tsofaffin hamayyar siyasar da suka daɗe suna addabar Kano, lamarin da ya samar da abin da ya bayyana a matsayin yanayin siyasa mai zaman lafiya.
“A yau a APC ta Kano, babu rikici ko saɓanin muradun siyasa. Dukkansu suna aiki tare cikin jituwa kamar iyali guda. Wannan ya faru ne saboda kyakkyawan shugabanci da diflomasiyyar Abba,” in ji shi.
Abba ya rage karfin siyasar ubangida
Suleiman ya ƙara da cewa matakin Gwamna Abba na zama da kafarsa a siyas bayan ya bar jikin Sanata Rabiu kwankwaso, ya rage karfin siyasar ubangida a Kano.
“Gwamna Abba ya rage karfin siyasar ubangida ta hanyar ballewa da kafa na shi tsarin, wanda hakan ya ’yantar da Kano daga duk wani nauyi.
"Ba kowa ne yake sarrafa shi ba; yana hulɗa da dukkan shugabanni a matsayin daidai da kowa. Wannan ne ya sa ake samun zaman lafiya," in ji shi.
Ya danganta ci gaban manyan ayyukan more rayuwa a sassan jihar da yanayin kwanciyar hankalin siyasar da aka samu.

Source: Facebook
Kwankwasiyya ta soki gwamnatin Kano
A wani labarin, kun ji cewa Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da takalar ’yan adawa yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Magoya bayan dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso sun kuma zargi gwamnatin Abba da hana yan Majalisar jam'iyyun adawa gudanar da ayyukansu.
Kungiyar Kwankwasiyya ta kuma soki kalaman da ta danganta ga Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a a wani shirin siyasa
Asali: Legit.ng

