Peter Obi Ya Yi Maganar Sayen Hannun Jari a Matatar Dangote, Ya ba 'Yan Najeriya Shawara
- Peter Obi ya yi tsokaci kan sayen hannun jari na matatar hamshakin attajiri, Aliko Dangote, wadda ke a birnin Legas
- IPO ɗin ya ƙunshi sababbin hannun jari biliyan 4.1, inda ake sayar da kowanne kan N525, mafi ƙarancin sayayya kuma hannun jari 10 ne
- Obi ya ce zuba jari a masana’antu zai taimaka wajen sauya tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da abin aka shigo da shi zuwa samar da kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓen 2027, Peter Obi, ya yi magana kan saka hannun jari a matatar Dangote.
Peter Obi ya ƙarfafa gwiwar ’yan Najeriya su saka jari a hannun jari a matatar hamshakin dan kasuwar.

Source: Facebook
Obi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026.
Ya ce ’yan Najeriya da dama da ke gida da ƙasashen waje sun nemi jin ra’ayinsa kan zuba jari a IPO ɗin.
Wace shawara Obi ya ba 'yan Najeriya?
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce bayan tattaunawarsa da ’yan Najeriya, mutane da dama sun tambaye shi ra’ayinsa game da IPO ɗin matatar Dangote.
“Yayin da nake ƙarfafa musu gwiwar su saya, ina so na bayyana cewa ina matuƙar alfahari da jajircewa da kuma nasarar zuba jarin Alhaji Aliko Dangote a fannin samar da kayayyaki na tattalin arzikin ƙasarmu.” In ji shi.
Obi ya ce zuba jarin Dangote ya ƙara tabbatar masa da buƙatar Najeriya ta sauya daga tattalin arzikin da ya fi karkata ga amfani da kayan da aka shigo da su zuwa wanda ya fi mayar da hankali kan samarwa a cikin gida.
Ya nemi kamfanonin Najeriya su zuba jari

Kara karanta wannan
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje
Obi ya kuma yi kira ga sauran ’yan kasuwar Najeriya da su mayar da hankali wajen zuba jari a ɓangarorin da ke samar da kayayyaki da ayyukan da za su bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce ya kamata kamfanoni su ba ’yan Najeriya damar mallakar wani kaso daga cikinsu ta hanyar sayar da hannun jari ga jama’a.
Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa ’yan ƙasa damar taka rawa wajen sake farfaɗo da masana’antun Najeriya.
Bayanan IPO na matatar Dangote
An bude sayar da hannayen jari na matatar Dangote a ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026. Shirin na IPO ya ƙunshi sababbin hannun jari guda biliyan 4.1, inda ake sayar da kowanne kan N525.
Mafi ƙarancin hannun jari da mutum zai iya saya shi ne guda 10, wanda darajarsu ta kai N5,250.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu
Jimillar kuɗin IPO ɗin ta kai N2.15 tiriliyan, kuma ana sa ran rufe sayar da hannun jarin ranar 13 ga Oktoba, 2026, bisa sharuddan da ke cikin takardar bayanin IPO ɗin.

Source: Facebook
Fadar shugaban kasa ta kalubalanci Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tsoma baki kan batun basussukan da Peter Obi ya bari bayan kammala wa'adin mulkinsa a jihar Anambra.
Fadar shugaban kasar ta ƙalubalanci Obi da ya cika alkawarinsa na daina yaƙin neman zaɓe idan aka tabbatar da cewa ya bar basussuka bayan ya bar mulki.
Asali: Legit.ng
