Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari Matsayin SGF

Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari Matsayin SGF

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da nadin tsohon minister Dakta George Akuma a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF
  • Hakan na zuwa ne jim kadan bayan nada Kakakin Majalisar Tarayya Mr Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban fadar ma'aikatan shugaban kasa
  • Shugaban na Najeriya kuma ya sanar da nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

Fadar Shugaban Kasa, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni, ya sanar da nadin tsohon Ministan Ayyuka Na Musamman, Dakta George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Tsohon gwamnan na jihar Benue ya yi aiki a karkashin gwamnatin Shugaba Kasa Muhammadu Buhari a matsayin ministan ayyuka na musamman.

Tinubu ya nada George Akume matsayin SGF
Tinubu ya nada tsohon minista, Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Hoto: Photo credit: Senator Dr. George Akume
Asali: Facebook

An tabbatar da nadin Dakta George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya (SGF)

Tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi, ne ya sanar da hakan cikin wata sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakon da Legit.ng Hausa ta gani ya ce:

"PBAT ya yi nade-nadensa na farko:
"Shugaban Fadar Ma'aikatan Shugaban Kasa, @femigbaja
"Mataimakin Shugaba Fadar Ma'aikatan Shugaban Kasa: Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa
"Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF): Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, George Akume.
"A al'adar Najeriya, Mataimakin Shugaban Fadar Shugaban Kasa yana yi wa mataimakin shugaban kasa aiki ne."

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace Ku Sani Game Da Ministan Buhari Da Tinubu Ya Nada SGF

A yau Juma'a 2 ga watan Yuni ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin Sanata George Akume, tsohon ministan harkokin na musamman a gwamnatin Buhari don zama Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Dakta George Akume kuma ya taba yin gwamna a jihar Benue a 1999 inda ya yi mulki na wa'adi guda biyu a jihar da ke arewacin Najeriya.

Bayan ya kammala wa'adinsa a matsayin gwamna a shekarar 2007, Akume ya yi takarar sanatan Arewa maso yammacin Benue, inda daga bisani ya zama shugaban masu rinjaye a majalisar a wani lokaci.

Baya gaza zarcewa a majalisa a 2019 ne Shugaba Buhari ya nada shi ministan ayyuka na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel