Biza: Amurka Ta Gano Makircin da Ake Shiryawa, Ta Aiko da Muhimmin Saƙo ga Yan Najeriya

Biza: Amurka Ta Gano Makircin da Ake Shiryawa, Ta Aiko da Muhimmin Saƙo ga Yan Najeriya

  • Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargadi masu neman biza kan gabatar da takardun bogi ko bayanan yaudara
  • Amurka ta ce za ta kai rahoton masu amfani da takardun bogi ga hukumomin tsaro da na gwamnati da abin ya shafa
  • Masu neman biza na bukatar su gabatar da sahihan takardu da bayanai domin kauce wa matsalolin neman bisa a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya gargadi masu neman biza kan amfani da takardun bogi ko bayanan yaudara.

Ofishin jaladancin ya sha alwashin cewa za a kai rahoton irin wadannan mutane ga hukumomin gwamnatin Amurka da abin ya shafa.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga manema labarai kan yakin Iran a fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Ofishin ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a matsayin wani bangare na kamfen dinsa na #VisaWiseTravelSmart.

Kara karanta wannan

Bayan abubuwa sun ɗauki zafi, an fito da gaskiyar shirin Atiku na dawo da tallafin mai a Najeriya

An kirkiro wannan shiri ne domin wayar da kan masu neman bisa kan yadda tsarin neman takardar izinin shiga Amurka yake.

Amurka ta dauki mataki

Ofishin Jakadancin ya ce jami’an kula da bayar da biza ba wai kawai suna kin amincewa da bukatar mutum ba ne idan suka gano takardun bogi ko bayanan da ke nuna cewa mai neman biza na iya zama barazana ga tsaro.

Ofishin ya ce idan jami’an sun gano takardun bogi ko wasu bayanai masu tayar da hankali, suna sanar da hukumomin gwamnatin Amurka da suka dace.

“Idan jami’an kula da bayar da biza suka gano takardun bogi ko suka gano bayanan da ke nuna cewa mutum na iya zama barazana, nan take muna sanar da dukkan hukumomin gwamnatin Amurka da abin ya shafa,” in ji ofishin.

Ya kara da cewa hukumomin na hadin gwiwa ne domin kare tsaron kasa da kuma hana masu aikata laifuffuka ko wasu miyagu shiga Amurka.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Takardun da ake dubawa

Wannan gargadi na nufin masu gabatar da takardun banki na bogi, takardun aiki na karya, bayanan tafiye-tafiye na karya ko wasu takardun tallafi na iya fuskantar matsaloli fiye da kin amincewa da bukatar bizar su.

Ofishin ya ce bayanan da aka gano yayin aikin tantance masu neman biza na iya kaiwa ga hukumomin tsaro da na tabbatar da doka na Amurka, a kokarin hana masu laifi da sauran mutane da ka iya zama barazana shiga kasar.

Fasfo.
Farfo na kasar Amuka lokacin da aka shirya shi don daukar hoto a birnin New York Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Gargadi ga masu neman biza

A baya, Ofishin Jakadancin Amurka ya sha jan hankalin ’yan Najeriya da ke neman visa domin yawon bude ido, kasuwanci, karatu ko hijira da su rika bayar da sahihan bayanai da takardun gaske yayin neman visa.

Saboda haka, an bukaci masu neman visa da su guji amfani da takardun bogi ko bayar da bayanan yaudara, domin hakan na iya shafar damar da za su samu ta yin nasarar neman bisa a nan gaba.

Kara karanta wannan

Yadda hukumar bogi ta yi ta yaudarar gwamnoni tana neman kudi da filaye

Kotun Amurka ta soke dokar Trump

A wani labarin kun ji cewa kotun Amurka ta soke dokar gwamnatin Trump da ta dakatar da bayar da bizar ga wasu ƙasashe har 75 ciki jar da Najeriya.

Alkalin kotun, Jeannette Vargas, ta ce dokar ta saba wa dokokin shige da fice na Amurka, domin ta wuce ikon ministan harkokin waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262