Yan Bindiga da Dama Sun Mutu da Suka Gamu da Bala'in da Ya Fi Karfinsu a Daji
- Rundunar ’yan sandan Kebbi ta ce an kashe ’yan bindiga da dama a dajin Gumki da ke yankin Kangiwa a jihar ta Arewa maso Yamma
- Sojoji da yan sanda ne suka hadu suka kai samame cikin dajin domin fatattakar ’yan bindiga da ’yan kungiyar Lakurawa
- Baya ga hallaka yan ta'addan, jami'an tsaro sun kwato bindigogin PKT da AK-47, harsasai, kayan sojoji da babura daga hannun ’yan bindigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, tare da haɗin gwiwar sojoji, ta ce sun kashe ’yan bindiga da dama a dajin Gumki da ke Kangiwa, ƙaramar hukumar Arewa ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda reshen jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Kebbi yau Litinin.

Source: Twitter
Yadda aka kashe yan bindiga a Kebbi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin yan sandan ya ce jami'an tsaro sun fafata da ’yan bindigar ne yayin wani samame da aka gudanar domin share dajin.
Sanarwar ta ce:
“Dajin Gumki sanannen wuri ne da ’yan bindiga da ’yan Lakurawa da ke aiki a yankin ke amfani da ita.”
Ya ce rundunar haɗin gwiwar sojoji da yan sanda ta yi nasarar fafatawa da ’yan bindigan tare da kashe da dama daga cikinsu yayin gudanar da samamen.
Jami'an tsaro sun kwato makamai
Sanarwar ta ƙara da cewa an kwato abubuwa da dama daga hannun ’yan bindigar, ciki har da bindiga kirar PKT guda ɗaya da harsasai masu hadari guda 174.
Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai 14, kayan soja guda biyu, takalman sojoji guda biyu, wayoyin hannu guda biyu, layu da Babura guda huɗu.

Kara karanta wannan
Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna
Sanarwar ta ce an dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ke ci gaba domin ƙara share yankin tare da kawar da miyagu daga jihar Kebbi gaba daya

Source: Twitter
Rundunar yan sanda ta nemi hadin kai
A cewar sanarwar, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Umar M. Hadejia, ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Ya ce wadannan ayyukan hadin gwiwa za su ci gaba ne bisa bayanan sirri domin yaƙi da ’yan bindiga, ta’addanci da sauran nau’o’in laifuffuka a jihar.
Rundunar ta buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai masu inganci cikin gaggawa domin daukar matakin da ya dace.
Sojoji sun ceto wata mata a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa sojojin Operation Fansan Yamma sun kubutar da wata mata da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da ita a jihar Kebbi a yayin da aka yi aikin ceto.
Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan rundunar ta samu sahihin bayanin sirri kan shirin biyan kuɗin fansar matar.
Asali: Legit.ng
