Binciken ICPC Ya Tono Yadda Hukumar Bogi Ta Shiga Kasafin Kudin Najeriya

Binciken ICPC Ya Tono Yadda Hukumar Bogi Ta Shiga Kasafin Kudin Najeriya

  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce Ofishin Kasafin Kuɗi bai tantance sahihancin hukumar PFIPC ba kafin shigar da ita cikin kasafin 2026.
  • PFIPC da aka tabbatar da cewa hukumar bogi ce ta nemi N3.85bn, amma daga baya aka ware mata N1.3bn a kasafin kuɗin tarayya na 2026
  • ICPC mai yaki da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa ba ta gano shaidar cewa an saki ko kashe N1.3bn da aka ware wa hukumar ba PFIPC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta soki Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya (BOF) game da rawar da ta taka a kan hukumar bogi ta PFIPC.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa ofishin kasafin kudi ya bari an shigar da wata hukumar da ake zargin ba ta wanzu bisa doka ba cikin kasafin kuɗin tarayya na 2026.

Kara karanta wannan

EFCC ta cika umarnin Tinubu, an bude asusun gwamnatin Osun

An bankado gazawar ofishin kasafin kudi kan hukumar PFIPC
Adeyemi Adeniyi da ya nada kansa shugaban PFIPC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Premium Times ta ruwaito cewa ICPC ta bayyana hakan ne a cikin rahoton bincikenta kan ayyukan hukumar da ake kira PFIPC da gwamnatin tarayya ta ce ba a kafa ta bisa doka ba.

Hukumar ICPC ta caccaki ofishin kasafin kudi

A ruwayar Politics Nigeria, Ofishin Kasafin Kuɗi ya aiwatar da tsarin shigar da hukumar cikin kasafin 2026 duk da cewa babu wasu muhimman takardu.

ICPC ta kara da cewa BOF bai gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da sahihancin dokar da ake cewa ita ce ta kafa hukumar ba.

Masu binciken sun gano cewa Ofishin Kasafin Kuɗin ya dogara ne da wata lambar gudanarwa da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF) ya bayar.

Haka kuma ofishin ya kara dogaro da wasu takardun kafa hukumar da aka danganta da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (OHCSF).

An gano gazawar ofishin kasafin kudin Najeriya

Sai dai ICPC ta ce BOF bai tabbatar da sahihancin waɗannan takardu da kansa ba, kuma bai tabbatar da cewa hukumar tana da ingantaccen tushe na doka ba.

Kara karanta wannan

Cibiyar BBYDI za ta horar da mata kan ilmin amfani da fasahar AI a Kaduna

ICPC ta ce ofishin kasafin kudi bai duba wasu muhimman takardu ba kafin amincewa da kasafin PFICP
Ofishin hukumar ICPC a Najeriya Hoto: ICPC
Source: Twitter

Hukumar bogin ta gabatar da buƙatar kasafin kuɗi a ranar 20 ga Agusta, 2025, inda ta nemi N3.85bn domin biyan albashin ma’aikata. An haɗa da faifan USB mai ɗauke da bayanan kuɗin da aka tsara kashewa wajen ma’aikata.

Ofishin Kasafin Kuɗi bai amince da adadin da aka nema ba. ICPC ta ce saboda babu tsarin albashi da Hukumar Kula da Albashi, Kuɗaɗen Shiga da Albashi ta Ƙasa ta amince da shi, jami'ai suka sake ƙididdige kuɗin ma'aikata ta amfani da tsarin albashin ma'aikatan gwamnati na haɗaka.

Hakan ya sa aka ware jimillar N1.3bn, wanda ya ƙunshi N802m na albashin ma'aikata, N200m na kuɗin gudanarwa da kuma N300m na manyan ayyuka.

Sai dai a rahoton na ICPC ta ce babu tabbacin an fitar da wadannan kudi ko kuma akasin hakan, yayin da ake sake samun karin bayanai game da hukumar bogin.

Bayanai sun fito kan hukumar PFIPC

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

A wani labarin, kun ji cewa Adeniyi Adeyemi ya ce ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun amince ko sun yi hulɗa da hukumar da ake takaddama a kanta.

Lauyoyinsa sun buƙaci a ba shi damar bayyana gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke bincike kan badakalar hukumar bogi ta PFIPC da ta jawo magana.

Sun ce fitar da rahoto ba tare da sauraron Adeyemi ba zai saɓa wa haƙƙinsa na samun adalci a binciken da ake yi na neman bayanai game da wadanda suke da hannu wajen kafa PFIPC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng