Dangote Ya Bayyana Babban Kuskurensa a Harkokin Kasuwanci da Ya Jawo Asarar Biliyoyi
- Aliko Dangote ya bayyana kuskuren da ya tafka a zuba jarin da ya ke yi a fannoni daban-daban na harkar kasuwanci
- Ya ce masana’antun nasa sun rufe ne sakamakon rashin isasshen kariyar manufofin gwamnati da kuma shigo da kayayyaki daga kasashen waje
- Dangote ya ce kusan ma’aikata 8,000 sun rasa ayyukansu, ciki har da 6,920 daga Nigerian Textile Mills da ke Ikeja, Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya fito ya bayyana babban kuskuren da ya taba tafkawa a harkokin kasuwanci.
Dangote ya bayyana zuba jarinsa a masana’antar masaku a matsayin babban kuskuren kasuwanci da ya taɓa yi a tsawon shekarunsa na kasuwanci.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da Arise News, inda ya yi tsokaci kan wasu ƙalubalen da ya fuskanta yayin da yake gina daular kasuwancinsa.

Kara karanta wannan
An fito da bayanin yadda duk wanda ya sayi hannun jarin matatar Dangote zai samu alheri
Wane babban kuskure Dangote ya yi?
Da yake magana kan harkar kasuwanci, Dangote ya ce: “Babban kuskurena a kasuwanci shi ne masana’antar masaku.”
Dan kasuwar ya ce daga bisani harkar ta durƙushe saboda rashin isasshen kariya daga manufofin gwamnati, tare da abin da ya bayyana a matsayin shigo da kayayyakin waje a kasuwar Najeriya.
Ya ce kayayyakin da ake shigo da su daga China da India sun yi wa masana’antun cikin gida illa sosai.
“An mamaye mu da kayayyakin da ake kawowa daga China da kuma India. Don haka daga ƙarshe sai da muka rufe masana’antun,” in ji Dangote.
Ma’aikata kusan 8,000 sun rasa ayyukansu
Dangote ya ce rufe masana’antun ya yi matuƙar tasiri kan ma’aikata, musamman waɗanda ke aiki a Nigerian Textile Mills da ke Ikeja, Legas.
Ya bayyana cewa kusan ma’aikata 8,000 ne suka rasa ayyukansu a faɗin harkokin masana’antar masaku.
Daga cikin adadin, ya ce ma’aikata 6,920 sun fito ne daga Nigerian Textile Mills da ke Ikeja kaɗai.

Kara karanta wannan
Dangote ya yi maganar samun yaron da zai gaje shi, ya fadi fatansa kan 'ya'yansa mata 3
“Mun sallami ma’aikata kusan 8,000 gaba ɗaya, ma’aikata 6,920 daga Nigerian Textile Mills da ke Ikeja kaɗai,” in ji shi.
Dangote ya koyi darasi
Dangote ya ce abin da ya faru ya koya masa darussa da suka taimaka wajen tsara yadda yake gudanar da zuba jarinsa a sauran harkokin kasuwanci.
Ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kamfani zai iya ci gaba da aiki cikin nasara ko da gwamnati ta janye kariyar da take ba shi daga baya.
Dangote ya ce darasin ya kasance muhimmin abu wajen tsara zuba jarin da ya sanya a sauran masana’antu da harkokin kasuwanci.

Source: Getty Images
Dangote ya yi magana kan tsadar fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa Aliko Dangote, ya danganta tsadar fetur a Najeriya da wasu dalilai, ciki har da ci gaba da fasa-kwaurin man zuwa ƙasashe makwabta.
Dangote ya ce farashin fetur a ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya ya fi na cikin gida da kashi 30 zuwa 50 cikin 100.
Asali: Legit.ng