Sanata Yari na Jagorantar Kamfen din Tinubu, Ya Yi Babban Rashi a Rayuwa
- Tsohon Gwamnan Zamfara kuma Sanata Abdulaziz Yari ya sanar da rasuwar gwaggonsa, Hajiya Rakkiya Jibrin, tana da shekaru 85
- Yari ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai karamci da kulawa, wadda ta samu ƙauna da girmamawa daga mutanen da suka san ta
- Ya roƙi jama’a da su tuna da ita a addu’o’insu, yana roƙon Allah Ya gafarta mata, Ya jiƙan ta, Ya ba ta Aljannar Firdausi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata Abdulaziz Abubakar Yari ya sanar da rasuwar gwaggonsa, Hajiya Rakkiya Jibrin, wadda ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.
Sanata Yari, wanda shi ne shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na 2027, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ya girgiza shi da sauran ’yan uwansa.

Source: Twitter
Yari ya bayyana irin halayen marigayiyar
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X ranar Laraba, 16 ga watan Satumban 2026.
A cikin saƙon ta’aziyyar da ya wallafa, Yari ya ce ya shiga cikin matsanancin baƙin ciki sakamakon rasuwar gwaggonsa.
Ya ce Hajiya Rakkiya mace ce mai kyakkyawar zuciya wadda ta kasance mai matuƙar kula da mutanen da ke kewaye da ita.
Ya ƙara da cewa karamcinta da kyautatawarta sun sa mutane da dama suka ƙaunace ta tare da girmama ta.
"Rasuwarta babban rashi ne a gare ni da gabadaya danginmu. Macece mai karamci wadda ta kula sosai da mutanen da ke tare da ita."
"Karamcinta da kyautatawarta sun sa mutane da dama suka ƙaunace ta tare da girmama ta." In ji shi.
A cewarsa, irin tasirin da ta yi a cikin al’ummarta zai ci gaba da kasancewa ko bayan rasuwarta.

Kara karanta wannan
Tinubu na ta samun goyon baya a Arewa, manyan malaman jami'o'i 600 sun bayyana matsayarsu
Ya miƙa al’amari ga Allah
Sanata Yari ya ce shi da iyalinsa sun miƙa wuya ga ƙaddarar Allah, tare da gode wa Ubangiji bisa rayuwar da Ya ba marigayiyar da kuma tsawon shekarun da suka samu damar kasancewa tare da ita.
Hakazalika tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya roƙi jama’a da su tuna da Hajiya Rakkiya a cikin addu’o’insu.
“Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya jiƙan ruhinta, Ya kuma ba ta Aljannar Firdausi."
“Allah Ya ba danginmu da dukkan waɗanda ke jimamin rasuwarta ƙarfin guiwar jure wannan babban rashi. Amin,” in ji Yari.

Source: Facebook
Sanata Yari ya yi magana kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa darakta-janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Abdulaziz Yari, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Yari ya ce babu wani dalilin da zai sa ’yan Arewa su ƙi goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya samu damar zama shugaban ƙasa da kuma sake lashe zaɓe.
Asali: Legit.ng
