Babbar Kungiyar Darika Ta Tsaida na Zaba tsakanin Uba Sani da Isa Ashiru a Kaduna
- Fityanul-Islamta yaba wa Gwamna Uba Sani saboda yadda ya kyale su wajen gudanar da harkokin addini
- Shugaban kungiyar ya jaddada cewa ba za su zabi wanda ke adawa da harkokin addini ko sha’anin almajiransu ba
- Sheikh Rabiu Abdullahi Zaria yana fatan gwamnan zai kammala zangonsa na farko kuma ya yi nasarar zarcewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Gwamna Uba Sani ya samu jinjina daga fitacciyar kungiyar addinin Musulunci gabanin zaben 2023.
A lokacin da wasu Musulmai musamman ‘yan darika suke murnar Mauludi, an sa masoyan Uba Sani cikin farin ciki.

Source: Facebook
Fityanul-Islam ta mara wa Uba Sani baya
Shugaban kungiyar Fityanul-Islam ya bayyana cewa suna tare da Uba Sani a zaben 2027, Leadership ta zo da labarin.
Sheikh Rabiu Abdullahi Zaria ya yi wannan bayani ne a wajen taron Maulidin da suka yi a filin Murtala Muhammad.

Kara karanta wannan
Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu
Malamin ya ce tunda Mai girma Uba Sani ya zama gwamna a Kaduna yake goyon bayan duk wasu ayyukan kungiyarsu.
Fityanul-Islam ta ce Sanata Uba Sani bai taba watsi da wata bukata daga gare ta ba don haka za su saka masa a 2027.
Da wa Fityanul-Islam ta ke adawa?
Rabiu Abdullahi Zaria yake cewa ba za su bada kuri’arsu ga wanda bai kaunarsu ba ko wanda zai hana su yin bikin Maulidi.
Bugu da kari, shugaban na Fityanul-Islam ya ce mabiyansu ba za su zabi wanda zai kama almajirai masu karatun Kur’ani ba.
Daily Trust ta rahoto cewa shehin ya yi wa Gwamna Uba addu’ar ya gama mulkinsa na farko lafiya kuma ya sake cin zabe.
Fityanul-Islam tana fata bayan wa’adi na biyu a Mayun 2027, gwamnan na Kaduna zai cigaba da samun daukaka a rayuwa.
Sheikh Rabiu ya ce suna fata a watan Mayu mai zuwa, za su sake taruwa a filin Murtala Muhammad a yi murnar nasarar APC.
Uba Sani ya je wajen Maulidi a Kaduna

Kara karanta wannan
Ganin sunan korarriyar minista da mutanen EFCC a kwamitin neman zabe ya jawo surutu
Taron d aka yi ya kunshi musulmai da kiristoci da kuma mutane daga kabilu dabam-dabam.
An ji shi kuma Uba Sani yana cewa dalilin yin Maulidi a Musulunci shi ne koyi da koyarwa da dabi’un Annabi Muhammad SAW.
A jawabin da ya yi wajen taron Maulidin, gwamnan ya ce sun hadu ne da nufin yin koyi da irin halin Manzon Allah SAW.
Sanata Uba ya kuma ce idan aka bi irin rayuwar Annabi , kasa gaba daya za ta zauna lafiya.
Hotunan Uba Sani a wajen maulidi.
Rikicin gwamnatin El-Rufai da almajirai
A sa’ilin da Nasir El-Rufai yake mulki, an rahoto gwamnatinsa ta kama almajiran makarantar Dahiru Bauchi lokacin da annobar COVID-19 ta yi kamari.
Shugaban makarantun Dahiru Bauchi a Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun shiga gidan da misalin ƙarfe 12:00 na dare.
Fatahu Pandogari ya tabbatar da cewa almajiran da aka ƙwace yara ne da ke zaune a gidan tun lokacin da gwamnati ta rufe makarantu saboda COVID-19
Asali: Legit.ng