Uba Sani: ‘Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

Uba Sani: ‘Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

  • Hukumar INEC ta ba Uba Sani a jihar Kaduna, amma zai kai kara kotun sauraron korafin zabe
  • Zababben gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar APC bai yarda da kuri’un da PDP ta samu ba
  • Sanata Uba Sani yana zargin akwai wuraren da ‘dan takaran PDP ya samu kuri’un rashin hankali

Kaduna - Zababben gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce zai kalubalanci sakamakon Gwamnan jihar Kaduna, ko da shi ne ya yi nasara a 2023.

Uba Sani ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da BBC Hausa a ranar Alhamis, ya ce akwai inda PDP tayi nasara da ratar da hankali ba zai dauka ba.

Sanata Uba Sani zai kalubalanci nasarar ‘dan takarar jam’iyyar PDP a wadannan wurare da aka ba shi ratar da yake ganin ba za ta yiwu a iya samunta ba.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Tashar talabijin Channels tace ‘dan takaran Gwamnan na APC kuma wanda zai gaji Malam Nasir El-Rufai yana ganin akwai inda aka samu kuri’un bogi.

Kuri'un PDP sun yi yawa?

Sani yana ganin ya kamata ratarsa da Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP ta zarce 10,806.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Cable ta ce zababben Gwamnan ya bada misali da karamar hukumar Chikun inda PDP ta samu kuri’u fiye da 89, 000, ya ce akwai alamar tambaya.

Uba Sani
‘Dan Takaran Gwamnan APC, Uba Sani Hoto: @Uba Sani
Asali: Twitter

Duk da zai kalubalanaci sakamakon zaben, Gwamna mai jiran gado ya ce zai yi wa kowa adalci – wadanda suka zabe shi har da wadanda ba su zabe shi.

Bisa zargin cewa magudi aka yi har jam’iyyar APC tayi nasara, Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya ce Ubangiji SWT ne Yake bada mulki ga wanda Ya so.

Kara karanta wannan

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

Rungumar kaddara a zabe

A hirar da aka yi da shi, ‘dan siyasar ya bada misali da zaben 2011 da ya fadi zaben Sanatan Kaduna t a tsakiya, ya ce a lokacin bai yarda ya tafi kotu ba.

Tribune ta rahoto tsohon Hadimin na Gwamna mai barin gado yana cewa Allah bai yi zai samu mulki ba sai a 2019 da ya zama Sanata a karkashin APC.

Wannan karo yana sa ran ya yi nasara a karar da zai shigar da PDP da ‘dan takararta a zaben gwamna.

Dattijo ya tafi kotu

Ana da labari Muhammad Sani Abdullahi da ya yi takarar Sanata a APC zai shigar da karar PDP da INEC a kan zaben da aka yi na ranar 25 ga watan Fubrairu.

'Dan takaran ya ce akwai saba doka, magudi da rashin bin tsarin dokar zabe da kin amfani da na’urar zabe da kuma amfani takardun boge a wasu mazabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng