Tinubu Ya Fitar da Sako g Masu Murnar Ranar Haihuwar Annabi Muhammad SAW a Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin musulmi zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW
- Tinubu ya bukaci Musulmi su yi koyi da sadaukarwa, hakuri, juriya da tawali’u na Annabi Muhammad SAW
- Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya su yi addu’ar kawo karshen rashin tsaro tare da taimakon marasa karfi a wannan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya musulman Najeriya murnar zagayowar Maulidin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare Shi).
Tinubu bukaci Musulmi a fadin Najeriya da su yi amfani da bikin Maulidin bana wajen sabunta kudurinsu na bin kyawawan dabi’un sadaukarwa, juriya, hakuri, tawali’u da son juna da Annabi Muhammad (SAW) ya yi wa duniya jagora da su.

Source: Facebook
Tinubu ya taya musulmi murna

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026.
Shugaban ya taya Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, yana mai cewa bikin bai kamata ya tsaya kan shagulgula kadai ba, illa ya kasance lokacin yin nazari, addu’a da tunani kan koyarwar Annabi SAW.
Tinubu ya ce ’yan Najeriya na da darussa masu yawa da za su koya daga rayuwa da halayen Annabi Muhammad (SAW).
Tinubu ya tunatar da Musulmi
Shugaban ya ce ya kamata Musulmi su yi kokari wajen bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman ta fuskar sadaukarwa, juriya, hakuri, tawali’u da rashin son kai.
“Ya kamata al’ummar Musulmi su yi kokari sosai wajen bin koyarwar Annabi Muhammad. Akwai manyan darussa na sadaukarwa, juriya, hakuri, tawali’u da rashin son kai da dukkanmu za mu iya koya daga rayuwar Annabi,” in ji Tinubu.
Ya kuma bukaci malamaibda su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Najeriya addu’a tare da karfafa wa mabiyansu gwiwa su mayar da darussan da suka koya daga rayuwar Annabi zuwa kokarin samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa.
Ya bukaci addu’ar zaman lafiya
Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya musamman da su yi addu’ar kawo karshen rashin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar wasu sassan kasar.
Ya kuma bukaci Musulman da ke gudanar da bikin Mauludi da su nuna koyarwar Annabi ta hanyar nuna tausayi da taimakon juna, musamman ga marasa galihu.

Source: Facebook
Shugaban ya ce ya kamata masu bikin su tallafa wa mabukata da wadanda ke cikin mawuyacin hali, saboda murnar bikin Mauludi.
Tinubu ya yi wa al’ummar Musulmi fatan kammala bikin Maulidin Annabi mai cike da zaman lafiya da albarkar addini.
An ba da hutun Maulidi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya Musulmai murna, tare da kira da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad
Asali: Legit.ng
