Wani Mutumi Ya Zare Bindiga, Ya Bude Wa Mutane Wuta a Wurin Bikin Aure a Jihar Kano
- Wani mutum mai shekaru 34, Rabiu Mukhtar ya bude wa mahalarta taron bikin aure a jihar Kano wuta, inda mutum daya ya mutu, uku suka jikkata
- Rahoton rundunar yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya fusata ne saboda hayaniyar kiɗa daga wurin bikin
- ’Yan sanda sun kama mutane biyu tare da kwato bindigar da ake zargin an yi amfani da ita, ana ci gaba da gudanar da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wani mutumi dan kimqnin shekaru 34, Rabiu Mukthar, ya bude wa mutane suna tsakiyar shagali a taron bikin aure a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ana zargin mutumin ya fito daga gidansa dauke da bindiga tare da bude wa mutane wuta saboda sun dame shi da kiɗa, inda mutum daya ya rasa ransa, yayin da wasu uku suka jikkata.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin, wanda ke zaune a Tudun Yola Quarters, ya fusata kan hayaniyar kida da ake yi a wajen bikin.
Yadda lamarin ya auku a Kano
Jami'in hulda da jama'a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Abubakar Kiyawa ya bayyana cewa wanda ake zargin ya fito daga gidansa sannan ya bude wuta kan mutanen da ke halartar bikin.
A cewar Kiyawa, Mukthar ya yi amfani da bindigar pump-action wajen harbin mutanen da ke wajen taron ba tare da nuna bambanci ba.
’Yan sanda sun kama mutum biyu
Abdullahi Kiyawa ya ce ’yan sanda sun gaggauta kai dauki bayan samun rahoton lamarin, inda suka kama Mukthar da wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya kara da cewa an kwato makamin da ake zargin an yi amfani da shi wajen harin daga hannun Mukthar.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Kakakin ’yan sandan ya kuma ce wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa wadanda suka shirya bikin kida ba su tuntube shi ba kafin gudanar da taron.
Hayaniyar kiɗa ta jawo harbin
A cewar Kiyawa, Mukthar ya kuma bayyana wa jami'an ’yan sanda cewa hayaniyar kida ta hana shi yin barci, lamarin da ya sa ya bude wuta kan mutanen da suka halarci bikin.
Ya ce a halin yanzu ana tsare da mutanen biyu a Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na rundunar yan sandan jihar Kano, CID, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.

Source: Facebook
An gurfanar da Maimuna a kotun Kano
A wani rahoton, kun ji cewa kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare wata budurwa mai suna, Maimuna Idris mai shekaru 25 a gidan gyaran hali bisa zargin yanke mazakutar saurayinta.
Maimuna, yar asalin karamar hukumar Maigatari ta jihar Jigawa , na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da yunkurin kisan kai da kuma jikkata mutum da rauni mai tsanani.
Lauyan masu gabatar da kara, H.A. Sani-Buhari, ya shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Yuli a Badawa Quarters da ke Kano.
Asali: Legit.ng
