Uba Sani Ya Zabi Kirista a Matsayin Wanda Zai Yi Masa Mataimakin Gwamna a 2027

Uba Sani Ya Zabi Kirista a Matsayin Wanda Zai Yi Masa Mataimakin Gwamna a 2027

  • Gwamna Uba Sani ya bayyana Kirista, Jerry Adams, a matsayin mataimakinsa a zaben gwamnan Kaduna na 2027 bayan tuntuba da nazari mai zurfi
  • Uba Sani ya ce zabin Adams ya nuna kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, hadin kai ba tare da la'akari da addini ko kabila ba
  • Gwamnan ya yabawa Jerry Adams kan gyare-gyaren da ya jagoranta a KADIRS da suka taimaka wajen bunkasa kudaden shiga a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaben shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya dauki matakin ne bayan gudanar da tuntuba da dama, nazari mai zurfi da kuma addu'o'i.

Kara karanta wannan

An goyi bayan harbe 'yan ta'adda da zarar an gan su ba tare da jiran izini ba

Gwamna Uba Sani ya zabi Jerry Adams a matsayin abokin takararsa a zaben 2027
Gwamna Uba Sani da Jerry Adams suna musabaha. Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Uba Sani ya zabi mataimaki a 2027

Uba Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 28 ga Yulin 2026.

Ya bayyana cewa zabin ba wai na neman mataimakin gwamna kadai ba ne, illa wata alama ce ta ci gaba da riko da manufofin hadin kai, adalci da bai wa kowa dama da gwamnatinsa ke bi tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

A cewar gwamnan, jihar Kaduna na da dimbin al'adu, addinai da kabilu, kuma wannan bambancin shi ne babban karfinta, ba abin da zai raba al'umma ba.

Ya ce gwamnatinsa ta shafe sama da shekaru uku tana kokarin dawo da zaman lafiya, karfafa amincewar jama'a ga gwamnati da kuma tabbatar da cewa ayyukan ci gaba sun isa dukkan kananan hukumomi 23 na jihar.

Ya kara da cewa an aiwatar da ayyuka a bangarorin hanyoyi, ilimi, lafiya, noma, samar da ruwa da walwalar jama'a bisa manufar cewa babu wata al'umma ko yankin da ya kamata a bari a baya.

Kara karanta wannan

Fitaccen mai barkwanci a Najeriya, AY ya daina zuwa coci, ya fadi abin da ya faru

Gwamna ya yabawa Jerry Adams

Uba Sani ya bayyana Jerry Adams a matsayin gogaggen jami'in gwamnati kuma kwararre a harkokin tara haraji, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya fasalin KADIRS zuwa daya daga cikin hukumomin tara haraji mafi inganci a Najeriya.

Ya ce karkashin jagorancin Adams, an inganta tsarin tattara kudaden shiga ta hanyar amfani da sabbin dabaru, gaskiya da kwarewa, lamarin da ya bai wa gwamnatin jihar damar kara zuba jari a fannin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da noma.

Gwamnan Kaduna ya zabi Kirista a matsayin abokin takararsa a zaben 2027
Taswirar jihar Kaduna, inda Uba Sani ya zabi Jerry Adams a matsayin abokin takara. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sakon gwamna ga al'ummar Kaduna

Gwamnan ya ce baya ga kwarewar Adams, ya kuma shahara wajen mutunci, tawali'u da kuma goyon bayan zaman lafiya da sulhu tsakanin al'ummomi.

Ya bukaci al'ummar Kaduna da su kalli wannan mataki a matsayin wani yunkuri na gina jihar da kowa zai samu damar ci gaba ba tare da nuna bambanci kan addini, kabila ko yanki ba.

Uba Sani ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaban gwamnatinsa, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa tare da hadin kan al'umma za su ci gaba da gina Kaduna mai cike da zaman lafiya, tsaro, adalci da ci gaba domin amfanin al'ummomi na yanzu da masu zuwa.

Kara karanta wannan

Matar aure ta kwarawa kishiyarta mai ciki ruwan zafi, ta haihu dan ya mutu

Uba Sani zai ajiye Muslmin Muslim

Tun da farko dama dai, Legit Hausa ta rahoto cewa, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yanke shawarar zaɓar Kirista daga Kudancin Kaduna a matsayin mataimakinsa.

Ana ganin matakin zai kawo daidaito tsakanin addinai, sabanin tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi amfani da shi a zaɓen 2019.

Majiyoyi sun ce gwamnan bai bayyana sunan wanda zai zaɓa ba tukuna saboda gudun rikice-rikice da matsin lamba daga 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com