Dakaru sun yi zuga, sun shiga gidan Dahiru Bauchi, sun yi gaba da Almajiransa

Dakaru sun yi zuga, sun shiga gidan Dahiru Bauchi, sun yi gaba da Almajiransa

- Dakarun Sojoji da ‘Yan Sanda sun shiga gidan Dahiru Bauchi sun dauki Almajirai

- Shugaban makarantun Shehin Malamin ya ce an auko masu ne cikin tsakar dare

- Majiyar ta ce har da wasu Jami’an KASTELEA na jihar Kaduna aka yi wannan aiki

Labarin da mu ka samu daga BBC Hausa shi ne jami’an tsaro sun shirya wata runduna wanda suka shiga gidan Sheikh Dahiru Bauchi a jihar Kaduna.

Wadannan dakaru ba su yi komai ba illa suka dauke almajiran da suke kwance a gidan wannan babban shehin malamin addinin musulunci, Dahiru Usman Bauchi.

Shugaban makarantun Sheikh Dahiru Bauchi da ke jihar Kaduna, Fatahu Umar Pandogari ya shaida wa BBC Hausa abin da ya faru a ranar Alhamis da safe.

Malam Fatahu Umar Pandogari wanda limamin wani masallaci mabiya darikar Tijjaniya ne a garin Kaduna, ya ce jami’an tsaro sun shiga gidan Shehin ne jiya.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi gwamnoni game da Almajirai

Ga abin da ya fadawa ‘yan jarida:

"Da misalin karfe 12:00 na tsakar dare, sojoji da ‘yan sanda da jami’an KASTELEA da dakarun FRSC suka shigo gidan Maulanmu Shehu (Dahiru Bauchi), suka kama almajirai suka tafi da su…”

A cewar Fatahu Umar Pandogari, babu wanda ya san dalilin kama wadannan Bayin Allah har zuwa yanzu.

Malam Umar Pandogari ya ce wadannan Almajirai suna zaune a gidan shehin ne tun lokacin da gwamnati ta sallami yaran makarantu saboda barkewar COVID-19.

KU KARANTA: COVID-19: A Bauchi zan yi tafsiri inji Dahiru Bauchi

Dakaru sun yi zuga, sun shiga gidan Dahiru Bauchi, sun yi gaba da Almajiransa
Shehin Malami Dahiru Bauchi a Aso Villa Hoto: Twitter Daga: @MBuhari
Source: Twitter

Shugaban makarantar ya ce yaran da aka tafi da su wadanda suke zaune ne a gidan Shehin ne, ba Almajiran da su ka zo karatu daga wasu wurare na daban ba.

Har zuwa yanzu, gwamnatin jihar Kaduna ba ta fito ta bayyana dalilin kama wadannan yara ba.

A lokacin da COVID-19 ta bulla, kun ji cewa babban malamin addinin musuluncin, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga jama’ar kasar da su bi umurnin likitoci.

Jagoran na mabiya Darikar Tijjaniyya a Najeriya ya bada fatawa ce mutane su daina musafaha a tsakaninsu domin guje wa kamuwa da cutar nan ta Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel