Sojojin Najeriya Sun Bindige Dan Bindiga har Lahira a Wani Artabu da Suka Yi

Sojojin Najeriya Sun Bindige Dan Bindiga har Lahira a Wani Artabu da Suka Yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Dakarun sojojin Operation Fansan Yamma sun ceto wani mutum da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna
  • Jami'an sojojin sun kuma dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai a jihar Sokoto, inda suka kashe ɗaya daga cikin maharan
  • A yayin samamen, sojojin sun kwato wayoyin hannu, kuɗi, katin ATM da katunan waya, kuma rundunar ta yi kira ga jama’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun ceto wani mutum da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna tare da dakile wani harin ta’addanci a jihar Sokoto.

An gudanar da ayyukan ne a ranakun 20 da 21 ga watan Agusta 2026, a wani bangare na ci gaba da kokarin rundunar na hana ’yan ta’adda samun damar gudanar da ayyukansu a yankin da take aiki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu dakarun Najeriya a jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Laftanar Kanal Aliyu Danja ya ce sun ceto wani mutum mai shekaru 43 da aka sace a kusa da garin Awon da ke karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Sojoji sun ceto wanda aka sace

Danja ya ce sojojin sun samu kiran gaggawa game da sace mutumin a ranar 20 ga watan Agusta, inda suka garzaya yankin domin bin sawun masu garkuwa da shi.

Ya ce sojojin sun bi sahun ’yan ta’addan har cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin, lamarin da ya tilasta masu barin wanda suka sace tare da tserewa.

Bayan ceto shi, sojojin sun mayar da mutumin ga iyalansa cikin koshin lafiya.

An bindige ɗan ta’adda a Sokoto

A wani samame da aka gudanar ranar 21 ga watan Agusta, sojoji tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron yankin sun mayar da martani kan wani harin da ’yan ta’adda suka kai kauyen Kwaren Gamba da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

Sanarwar ta ce sojojin sun yi artabu da maharan tare da tilasta masu ja da baya cikin rudani. A yayin da sojojin ke binsu domin hana su tserewa, an samu nasarar kashe ɗaya daga cikin ’yan ta’addan.

Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kwato wayoyin hannu

Bayan kashe ɗan ta’addan, sojojin sun kwato wasu kayayyaki da suka haɗa da wayoyin hannu guda biyu, kuɗi, katin ATM da katunan waya.

Sahara Reporters ta ce rundunar ta ce samamen wani bangare ne na ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda domin hana su samun damar kai hare-hare ko kafa sansanonin ayyukansu.

Danja ya ce sun kuduri aniyar ci gaba da ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro domin samar da yanayi mai aminci ga al’ummomin yankin.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abin da suka ga yana da alaƙa da ayyukan ’yan ta’adda ga jami’an tsaro cikin gaggawa.

An sace masallata a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu masallata da suka halarci sallar Juma’a a babban masallacin garin Dekara da ke karamar hukumar Borgu ta jihar Niger sun fada hannun ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi barin wuta kan yan ta'adda, miyagu da dama sun rasa rayukansu

Wani mazaunin yankin, Mohammed Haruna, ya ce maharan sun sace masallatan ne jim kadan bayan kammala sallar Juma’a da furta “Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh”.

Ya ce ’yan bindigar sun kewaye masallacin tare da tafiya da masallatan cikin daji, inda ake zargin sun nufi dajin Kainji da ake zaton yana daga cikin wuraren da ’yan bindigar ke fakewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng