Hanyoyi 4 Na Haɗa NIN, BVN da Asusun Banki Cikin Sauƙi: “Yau Ce Ranar Karshe”

Hanyoyi 4 Na Haɗa NIN, BVN da Asusun Banki Cikin Sauƙi: “Yau Ce Ranar Karshe”

  • Bankunan Najeriya sun himmatu wajen tabbatar da cewa duk kwastomominsu sun hada BVN da NIN da asusun ajiyarsu
  • Manufar ita ce inganta tsaro a ayyukan banki da tabbatar da bin ka'idojin amfanin da bankunan na kasa
  • Wannan matakin zai taimaka wajen rage ayyukan barayin intanet, 'yan damfara da kutse a asusun banki ba da izini ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Babban bankin Najeriya ya umurci duk abokan huldar bankuna da su hada lambar su ta kasa (NIN) da kuma lambar tantance bankin (BVN) zuwa asusun bankinsu.

CBN, NIN, Bankuna
Bayani dalla-dalla kan sauƙaƙan matakai na yadda ake haɗa NIN, BVN ɗin ku da asusun banki. Hoto: BusinessDay, NIMC discussion group, NewsWire NGR
Asali: Facebook

Idan za a iya tunawa, CBN ya fara ba da umarnin ne a wata takarda da ta fitar a ranar 1 ga Disamba, 2023, da nufin saka takunkumin tsaro kan asusun bankuna.

Kara karanta wannan

Yan wasan ƙwallon ƙafa 5 da aka dakatar da su saboda sun yi amfani da ƙwayar ƙarin kuzari

Menene NIN da BVN da amfanin su?

Yayin da wasu bankunan suka saka ranar 29 ga Fabrairu, 2024, a matsayin ranar ƙarshe na rufe hadawar, wasu kuma sun yi shiru ba tare da fadin wa'adi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NIN ta ƙunshi lambobi 11 waɗanda ake alakanta su da mutum bayan ya kammala rajista a shafin rijistar zama dan kasa (NIDB).

Lambar BVN wata fasaha ce da ke aka samar da ita domin tantancewa tare da adana bayanan mutum da nufin samar da tsaro gare shi a hada-hadar kudi ta bankuna.

Bankuna sun nemi abokan hulda suyi biyayya

Bankunan Najeriya sun sanar da kwastomominsu bukatar sabunta bayanan asusun bankinsu da BVN da NIN kafin ranar Juma’a 1 ga Maris, 2024.

Bankunan sun yi gargadin cewa kwastomomin da suka kasa hada BVN, NIN din su na iya rasa asusun ajiyarsu.

Kara karanta wannan

Babban labari: Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an manhajar Binance, an samu ƙarin bayani

Yadda ake hada NIN/BVN da asusun banki

Don haɗa BVN ko NIN ɗin ku da asusun ajiyar ku na banki, kuna iya amfani da ɗaya daga wadannan hanyoyin:

Ta hanyar SMS

Kawai rubuta BVN/NIN, lambar asusunka, da lambar BVN/NIN zuwa lamba/lambar da layin ka ko banki ya bayar.

Ta hanyar shafin bankin a intanet

Ka shiga cikin shafin bankinka na intanet don hada wa.

Ka latsa bangaren BVN/NIN.

Danna 'new request' tare da shigar da lambobin BVN/NIN din ka. Zaɓi bankin da aka yi maka BVN/NIN ɗin, amsa tambayoyin sirri tare da bin matakan da aka nuna maka.

Ta hanyar sakon 'email'

Ka aika bukatar hakan zuwa ga jami'in asusun bankinka ta hanyar 'email.'

Ziyarci bankin ka

Ziyarci reshen bankinka mafi kusa domin ƙarin bayani kan sabunta bayanan.

CBN zai rufe asusun bankin da ba a hada shi da BVN

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa bankin CBN ya ba dukkan masu asusun banki a kasar da su hada lambar BVN dinsu da asusun su don rage yawaitar masu damfara.

CBN ya umarci bankunan Najeriya da su kulle asusun bankunan duk wanda ya ki hada asusun da BVN dinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel