Bayan Gargadin DSS, Sojoji Sun Rika Aman Wuta a kan Yan Bindiga a Sokoto
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ƙara yawan hare-haren sama kan ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma
- Rundunar ta ƙara yawan jiragen yaƙi da sa ido a Jihar Sokoto domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa na jami’an tsaro da ke kokarin kakkabe taaddanci
- Shugaban Rundunar Sojin Sama ya ce za a ci gaba da amfani da bayanan sirri da ƙarfin jiragen sama wajen dakile ayyukan masu laifi tare da kare fararen hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ƙara tsaurara hare-haren sama da take kai wa ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 24 ga watan Agusta, 2026 a Abuja kwanaki kadan bayan DSS ta ce akwai barazana kan manyan makarantu a Sokoto.

Source: UGC
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Ejodame ya ce ƙara yawan ayyukan jiragen sama a Jihar Sokoto na daga cikin matakan tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa da jami’an tsaro ke gudanarwa a yankin.
Sojoji sun kai hari ta sama a Sokoto
The Nation ta kawo labarin cewa Ejodame ya ce ƙarfafa yawan sojojin sama da ayyukansu na da matuƙar muhimmanci wajen tunkarar barazanar tsaro.
Ya ce an gano ’yan ta’adda da ’yan bindiga kan yi amfani da wurare masu wahalar shiga da buya domin kauce wa jami’an tsaro na ƙasa.
Ana ganin matakin ya nuna aniyar rundunar na ci gaba da matsa wa masu tayar da hankali lamba, ƙara sa ido daga sama da kuma samar da damar mayar da martani cikin gaggawa a yankunan da ake gudanar da ayyukan haɗin gwiwa.
Sojojin sama sun matsa wa yan bindiga
Ya ce hakan zai kuma hana ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka samun damar yin zirga-zirga cikin sauƙi tare da samar wa sojojin ƙasa damar ƙarfafa nasarorin da suka samu.

Source: Original
Ejodame ya nakalto Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, yana cewa NAF za ta ci gaba da inganta yadda take amfani da ƙarfin jiragen sama domin samar da gagarumar nasara wajen tallafa wa ayyukan haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Ya ce sauyin yanayin tsaro na buƙatar samun bayanan sirri a kan lokaci, amfani da ƙarfin jiragen sama cikin sauri da kuma haɗa kai sosai tsakanin sojojin sama da na ƙasa.
Ya ce:
“Manufarmu a bayyane take: mu ci gaba da matsa wa masu aikata laifuka lamba, hana su ’yancin aiwatar da ayyukansu, tare da samar da yanayin da zai bai wa sojojin ƙasa damar mamaye wuraren da ake gudanar da ayyuka.”
'Yan bindiga sun kai hari Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa masu garkuwa da mutane sun kashe wasu mazauna kauyen Abu biyu yayin da suke kokarin tserewa da likita da matar Hakimi da suka sace.
Sojojin Operation Enduring Peace sun kaddamar da farmaki da aikin ceto domin kubutar da wadanda aka sace a karamar hukumar Sanga ta Kaduna.
An gano matakin da jami'an sojin suka dauka a kokarin ceto matar da likitan da a yanzu haka ke tare da yan bindigar da suka kai harin wanda ya gigita mazauna yankunan.
Asali: Legit.ng


